An bi diddikin karyar da Shugaban Amurka Trump yayi a kan mulki

An bi diddikin karyar da Shugaban Amurka Trump yayi a kan mulki

Wani bincike da aka yi ya nuna cewa ba sau daya ko biyu ba, shugaban kasar Amurka watau Donald Trump ya saba zagewa ya shirga karya ga mutanen Amurka da kuma daukacin al’ummar Duniya.

Jaridar nan ta kasar Amurka mai suna Washington Post ta rahoto cewa Donald Trump ya fadi abubuwan da ba gaskiya ba, ko kuma kalaman da ke da jurwaye kamar wanka akalla sau 9, 014 a cikin kwanaki 773 da yayi a kan kujerar mulki.

A farkon makon nan ne Donald Trump din ya cika kwanaki 773 a kan karagar mulkin kasar Amurka. Binciken da aka gudanar ya nuna cewa kusan a shekarar 2019, Trump ya kan jibga irin wadannan karyayyaki sau 22 a kullum.

KU KARANTA: Wani babban Attajirin Duniya ya kira Trump da dakiki

An bi diddikin karyar da Shugaban Amurka Trump yayi a kan mulki
Shugaba Trump ya saba fadawa mutanen Amurka abin da ba daida ba
Asali: UGC

Binciken kwa-kwaf din da aka yi a Amurka ya tabbatar da cewa idan aka tattara komai aka yi lissafi, a shekarar farko da Trump ya hau mulki, abubuwan da yake fada da ba su tabbata gaskiya ba, ba su wuce 5.9 a duk ranar Duniya.

Sai dai abin da Donald Trump yana cigaba da yin gaba ne a kullum inda aka fahimci cewa a shekarar bara, ya kan yi karya akalla sau 16.5 a kullum. Donald Trump ya kan zage ne ya hakikance a kan cewa lallai gaskiya yake fada.

KU KARANTA: Dangote ya fi duk wani Bakar fata dukiya a Duniya

Yawanci shugaban kasar ya kan fadi abubuwan da ba su inganta bane a wajen taron gangamin siyasa ko kuma a kan shafin sa na sadarwa na zamani na Tuwita. An gano dai cewa babu gaskiya a cikin 1 bisa 4 maganar shugaba Trump.

Binciken da Washigbton Post tayi, ya tabbatar da cewa daga cikin manyan abubuwan da shugaba Donald Trump ya kuma ba gaskiya bane akwai cika bakin da yake yi na batun samawa jama’a aiki da kuma habaka tattalin Amurka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel