'Yan bindiga kai hari dakin ajiyar kaya, sun kashe dan sanda

'Yan bindiga kai hari dakin ajiyar kaya, sun kashe dan sanda

Wasu gungun 'yan bindiga da ba gano ko su wanene ba sun kai farmaki wani gidan ajiye kaya da ke Aba na jihar Abia inda suka kashe jami'in dan sanda guda da ke aiki tare da rundunar 'yan sanda na Aba.

Wata majiya ta ce dan sandan da aka kashe ya shahara a unguwar inda ake masa lakabi da Nma Agha (Takobin Yaki).

The Nation ta gano cewa kafin harin, 'yan bindigan sun tafi wani dakin ajiya da ke unguwar Clifford a karamar hukumar Aba ta Kudu inda su kayi sace kaya kuma suka kwace kudade masu yawa daga hannun masu shaguna.

Wasu rahottanin da ba a tabbatar ba sun ce 'yan bindigan sun harbe wani ma'aikaci amma daga bisani an garzaya da shi asibiti a East road inda yana karbar magani bayan ya zubar da jini sosai.

DUBA WANNAN: Gwamna Bagudu ya yi rashin shakikinsa

'Yan bindiga sun kai farmaki dakin ajiyan kaya, sun kashe dan sanda daya
'Yan bindiga sun kai farmaki dakin ajiyan kaya, sun kashe dan sanda daya
Asali: UGC

Sai dai wasu na fargaban cewa ma'aikacin ba zai yi rai ba.

An gano cewa 'yan bindigan sun gama fashi ne kuma suna hanyarsu ta tafiya sai su kayi karo da tawagar 'yan sandan kuma suka bude wuta kuma suka harbi jami'in dan sandan.

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Abia, Geoffrey Ogbonna ya tabbatar da afkuwar lamarin tare da rasuwar dan sandan inda ya ce an fara gudanar da bincike domin gano ko su wanene suka aikata mummunan aikin.

Ogbonna ya ce 'yan sandan sun fara neman 'yan bindigan domin a tabbatar cewa ba su tsere ba.

A bangarensu, mazauna Aba sun bayyana fargabarsu a kan irin hare-haren da ake kaiwa masu shaguna da jami'an tsaro musamman a garin Aba inda suka ce ya kamata a dauki mataki a kai.

Wani jami'in tsaro da ya nemi a boye sunansa ya bayyanawa majiyar Legit.ng cewa irin wannan laifukan sun saba faruwa idan lokacin zabe ya karato.

A cewar dan sandan, 'yan bindigan musamman wanda ke yiwa 'yan siyasa aiki sukan yiwa al'umma fashi domin su samu kudin sayan makamai idan kuma hakan bai yiwa ba sukan kai wa jami'an tsaro hari.

Ya kuma ce suna iya kokarinsu domin tabbatar da cewa sun takawa 'yan bindigan birki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel