Da duminsa: Wasu mutane cikin kayan soji sun yi kutse fadar Ateke

Da duminsa: Wasu mutane cikin kayan soji sun yi kutse fadar Ateke

Wasu mutane sanya da kayan sojoji sun kai farmaki fadar Ateke Tom, Amanyanabo na masarautar Okochiri da ke karamar hukumar Okrika na jihar Rivers.

Mutanen sun shiga fadar sannan sun bincike dakunan da ke fadar.

A halin yanzu dai ba a san dalilin da ya sa suka kai sumamen a fadar basaraken ba.

Wannan dai yana zuwa ne kwanaki kadan gabanin zaben gwamna da 'yan majalisun jiha da za a gudanar a jihar a ranar Asabar.

DUBA WANNAN: Dan takarar APC da ya fadi zaben kujerar majalisar wakilai ya koma PDP

Da duminsa: Wasu mutane cikin kayan soji sun yi kutse fadar Ateke
Da duminsa: Wasu mutane cikin kayan soji sun yi kutse fadar Ateke
Asali: UGC

Tom Ateke, tsohon shugaban 'yan kungiyar masu tayar da kayan baya ya rungumi shirin gwamnati na yafewa masu tayar da kayan baya ne tun a shekarar 2008 tare da mayakansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel