Mai Martaba Sa’ad Abubakar III ya nemi a shiga neman Watan Rajab

Mai Martaba Sa’ad Abubakar III ya nemi a shiga neman Watan Rajab

Sarkin Musulmi Mai Martaba Alhaji Sa’ad Abubakar III, yayi kira ga Musulman kasar nan da su fara neman wata a daren nan. Mun samu wannan labari ne a jiya Laraba 6 ga Watan Maris na 2019.

A jiya Sultan Sa’ad Abubakar III ya nemi jama’a su zura idanu domin ganin jinjirin Watan Rajab mai shirin kamawa. Sarkin Musulmin yayi wannan kira ne ta bakin mai taimakawa majalisar san sa a kan harkokin addinin musulunci.

A jawabin da ya fito daga bakin Farfesa Sambo Shuaibu a fadar ta Sarkin Musulmi, an nemi al’umma su sa-ido domin dacewa da jinjirin wata mai zuwa na Rajab na shekarar nan ta 1440 ganin cewa an kawo karshen wannan watan na yau.

KU KARANTA: Wani Malami ya bayyana yadda ya hango nasarar Buhari tun kafin zabe

Mai Martaba Sa’ad Abubakar III ya nemi a shiga neman Watan Rajab
Sultan na kasar Sokoto Sa’ad Abubakar III yace yau za a duba watan Rajab
Asali: UGC

Yau ne dai Ranar 29 ga Watan 6 na Jimadal Akhir, don haka za a fara bidar shigowar watan Rajab. Sarkin Musulmin ya nemi duk wanda ya ga sabon watan da ya fadakar da babban Hakimin yankin sa ko kuma Lawanin kauyen da yake.

Idan an sanar da masu unguwanni da Sarakuna ne dai, Sarkin Musulmi zai samu labari domin a sanar da jama’a cewa an shiga sabon wata. A wannan wata ne dai da za a shiga watan da wasu kan yi azumin da ake kira na tsofaffi a Yankin nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel