Jam’iyyar PDP ta rasa wasu manyan mambobinta inda suka koma APC

Jam’iyyar PDP ta rasa wasu manyan mambobinta inda suka koma APC

Guguwar sauya sheka ya kai ziyara jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a jihar Ekiti yayinda manyan mambobin jam’iyyar suka koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Masu sauya shekar sun samu jagorancin tsohon dan majalisar dokokin tarayya, Sanata Bode Ola, wanda ya wakilcin yankin Ekiti ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 2009 da 2011 da kuma wani tsohon mamba a majalisar wakilai (2003-2007), Hon. Segun Ola, da magoya bayansu.

Manyan jiga-jigan na PDP biyu ssun samu tarba a APC daga wajen mataimakin gwamna, Otunba Bisi Egbeyemi a wani gagarumin gangami da ya gudana a yankin Okeyinmi da ke Ekiti a yammacin ranar Laraba, 6 ga watan Maris.

Jam’iyyar PDP ta rasa wasu manyan mambobinta inda suka koma APC
Jam’iyyar PDP ta rasa wasu manyan mambobinta inda suka koma APC
Asali: Twitter

Tsohon sanatan ya kasance tsohon Shugaban makarantun firamare (SUBEB) a gwamnatin tsohon gwamna Ayo Fayose.

KU KARANTA KUMA: Shugabannin Fulanin PDP 66 da mabiyansu 1000 sun koma APC gaab da zabe

Tsohon Shugaban SUBEB din yace ya koma APC ne saboda ci gaban da gwamnatin Gwamna Kayode Fayemi ta kawo jihar wanda ya inganta rayuwar mutanen jihaar cikin watanni hudu da hawansa kujerar gwamna.

A nashi bangaren, tsohon dan majalisa, Ola ya bayyana cewa kirarin kamfen din Fayemi na mayar da jihar kan martabarta ne ya ja ra’ayin shi zuwa jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel