Kotun daukaka kara ta tabbatar wa da Abba gida gida takarar sa

Kotun daukaka kara ta tabbatar wa da Abba gida gida takarar sa

Za a fafata da dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, a zaben gwamnoni da mambobin majalisar dokoki da za a yi ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

A wani hukunci da kotun daukaka kara ta kara ta yanke a yau, Alhamis, kotun ta dakatar da hukuncin da kotun farko ta yanke na umartar hukumar zabe ta kasa (INEC) a kan ta cire sunan dan takarar jam’iyyar PDP daga cikin jerin ‘yan takarar gwamna da za su fafata a zaben neman kujerar gwamnan jihar Kano.

A ranar Litinin ne Jastis Lewis Allagoa na babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Kano ta yanke hukuncin a hana PDP shiga zaben saboda jam’iyyar ba ta gudanar da zaben fidda ‘yan takara bisa ka’ida ba.

Kotun daukaka kara ta tabbatar wa da Abba gida gida takarar sa
Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Ali Amin-Little, daya daga cikin wadanda su ka nemi jam’iyyar PDP ta tsayar da su takarar gwamna a jihar Kano ne ya shigar da karar kalubalantar tsayar da Abba a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP.

DUBA WANNAN: Ban mutu ba, ina nan da rai da lafiya ta – Matashin da ya yi iyo a kwata saboda Buhari

A ranar 2 ga watan Oktoba na shekarar 2018 ne aka bayyana cewar Abba, surukin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, a matsayin wanda ya kasha zaben cikin gida da PDP ta yi da adadin kuri’u 2,421 yayin da mai biye ma sa, Jafar Sani Bello, ya samu kuri’u 1,258.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel