Yanzu Yanzu: APC na samu Karin karfi yayinda Gbenga Daniel na PDP ya umurci magoya bayansa da su zabi Dapo Abiodun

Yanzu Yanzu: APC na samu Karin karfi yayinda Gbenga Daniel na PDP ya umurci magoya bayansa da su zabi Dapo Abiodun

Wani tsohon gwamnan jihar Ogun kuma darakta Janar na kungiar kamfen din takarar shugabancin Atiku ABubakar, Otunba Gbenga Daniel ya umurci magoya bayan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Remo, jihar Ogun da su zabi dan takarar gwamna na jam’iyar All Progressives Congress (APC), Dapo Abiodun, a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa Daniel ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya saki a ranar Alhamis,7 ga watan Maris.

Legit.ng ta tattaro cewsa Sanata Buruji Kashamu ya kasance dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP wanda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta shaida a zaben.

Yanzu Yanzu: APC na samu Karin karfi yayinda Gbenga Daniel na PDP ya umurci magoya bayansa da su zabi Dapo Abiodun
Yanzu Yanzu: APC na samu Karin karfi yayinda Gbenga Daniel na PDP ya umurci magoya bayansa da su zabi Dapo Abiodun
Asali: UGC

An tattaro cea takarar Kashamu, wanda wata kotu ta tabbatar a watan Janairu, bai samu karbuwa ba wajen shugabannin jam'iyyar na kasa, wanda ya gabatar da Ladi Adebutu a matsayin zabinsu a jihar.

Wata kotu a ranar Laraba, 6 ga watan Maris ta sake tabbatar da takarar Kashamu.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Sokoto ta tura dalibai 50 kasar Ukraine domin karatun Likitanci

A baya Legit.ng ta rahto cewa Guguwar sauya sheka ya kai ziyara jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a jihar Ekiti yayinda manyan mambobin jam’iyyar suka koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Masu sauya shekar sun samu jagorancin tsohon dan majalisar dokokin tarayya, Sanata Bode Ola, wanda ya wakilcin yankin Ekiti ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 2009 da 2011 da kuma wani tsohon mamba a majalisar wakilai (2003-2007), Hon. Segun Ola, da magoya bayansu.

Manyan jiga-jigan na PDP biyu ssun samu tarba a APC daga wajen mataimakin gwamna, Otunba Bisi Egbeyemi a wani gagarumin gangami da ya gudana a yankin Okeyinmi da ke Ekiti a yammacin ranar Laraba, 6 ga watan Maris.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel