Sakamakon Zabe: Buhari ya gurɓata Kotun Koli, ba bu lallai Atiku ya cimma nasara - Agbakoba

Sakamakon Zabe: Buhari ya gurɓata Kotun Koli, ba bu lallai Atiku ya cimma nasara - Agbakoba

A yayin da dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ke ci gaba da kalubalantar sakamakon babban zaben kasa, wani babban Lauya, tsohon shugaban kungiyar Lauyoyin Najeriya, Dakta Olisa Agbakoba, ya ce ba bu lallai ya samu nasara.

Tsohon shugaban kungiyar Lauyoyin Najeriya ta NBA, Dakta Olisa Agbakoba (SAN), ya bayyana goyon bayan sa ga dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, wajen kalubalantar sakamakon babban zaben kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.

Yayin bayyana goyon bayan sa ga Atiku, Dakta Agbakoba cikin tantama da shakku ya ce ba bu lallai Atiku ya cimma nasara a shari'ance sakamakon yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gurɓata Kotun Kolin ta Najeriya.

Sakamakon Zabe: Buhari ya gurɓata Kotun Koli, ba bu lallai Atiku ya cimma nasara - Agbakoba
Sakamakon Zabe: Buhari ya gurɓata Kotun Koli, ba bu lallai Atiku ya cimma nasara - Agbakoba
Asali: Depositphotos

Dakta Agbakoba ya bayyana cewa, hukuncin shugaban kasa Buhari na dakatar da Alkalin Alkalai na kasa, Mai Shari'a Walter Onnoghen, ya sanya wata shimfida ta rashin gaskiya da kulla tuggu a hukumar Shari'ar kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, makonni kadan gabanin babban zabe, shugaban kasa Buhari ya dauki hukuncin dakatar da Alkalin Alkalai na kasa, inda ya maye gurbin sa da mukaddashi, Mai Shari'a Muhammad Tanko.

KARANTA KUMA: Kotu ta hana Atiku amfani da kimiyyar zamani wajen binciken kayayyakin zabe

Bisa ga madogara ta wannan dalili da kuma kwarewar sa a fannin shari'a musamman dambarwa ta rashin amincewa da sakamakon zabe, Dakta Ogbakoba tun a baya ya bayyana yadda rashin adalci zai yiwa Atiku shinge da kuma iyaka ta samun nasarar kan kudirin sa.

Yayin da tsohon mataimakin shugban kasa ke ci gaba da tayar da balli kan wannan lamari, a jiya Laraba kotun sauraron korafe-korafen zabe ta umarci hukumar zabe ta kasa wato INEC da ta mika masa kayayyakin da ta ribata wajen gudanar da zabe domin aiwatar da binciken sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel