Daga karshe: Kotu ta shirya yanke hukunci ga matar da ta bankawa mijinta wuta

Daga karshe: Kotu ta shirya yanke hukunci ga matar da ta bankawa mijinta wuta

Amina Dauda, matar da ta ake zarginta da kashe mijinta, Mohammed Matazu, wani dan jarida da ke aiki da FRCN, rediyon Kaduna, ta hanyar banka masa wuta, za ta san makomarta a ranar 30 ga watan Mayu.

Dauda, mai shekaru 28, ta gurfana ne gaban mai shari'a Hussein Baba-Yusuf, a ranar 22 ga watan Mayu, 2013, akan zarginta da aikata laifuka 3 da suka hada da kisan kai, wanda ke da hukuncin kisa.

KARANTA WANNAN: Asiri ya tonu: Mun gano shirin gwamnatin tarayya na tafka magudi a jihohi 24 - CUPP

Musa ya bukaci kotun da ta yanke hukunci akan wacce ake zargi, yana mai cewa shaidu biyar da aka gabatar gaban kotun ya bayar da dukkanin hujjojin da ake bukata da suka tabbatar da cewa wacce ake zargin ceta aikata laifin.

Jami'i mai shigar da karar, ya ce wacce ake zargin ta watsawa mijinta fetur a cikin gidansa da ke Gwarinpa, Abuja, a ranar 7 ga watan Fabreru, 2013 inda nan take ta cinna masa wuta, wanda ya mutu kafin a karasa da shi asibiti sakamakon munanan raunukan da ya ji.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel