Da duminsa: Wajibi ne PDP ta yiwa yan Najeriya bayani kan arzikin da tayi watanda - Buhari

Da duminsa: Wajibi ne PDP ta yiwa yan Najeriya bayani kan arzikin da tayi watanda - Buhari

Wajibi ne Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yiwa yan Najeriya bayanin yadda tayi almubazzarancin makudan dukiyoyi da ta samu daga cinikin man fetur tsakanin 1999 da 2014, shugaba Muhammadu ya jaddada.

Yayinda ya karbi bakuncin kungiyar kwadagon Najeriya da suka kawo masa ziyarar taya murna kan nasarar da ya samu a zabe a fadar shugaban kasa ranar Alhamis, shugaban kasa ya laburta cewa gwamnatinsa ta samu abubuwa a mace a 2015.

Saboda haka, ya zama wajibi a tambayi jam'iyyar da ke kan mulki na tsawon shekaru 16 abinda tayi da kudin da kasar ta samu na cinikin man fetur.

Yace: "PDP ba tayi bayanin abinda tayi da kudin ba. Babu hanyoyi, babu layin dogo, babu wutan lantarki. Sunce sun kashe $16 bilion kan wuta, amma ina wutar take?"

"Basu yi bayani wannan almubazzaranin da sukayi ba kuma yan Najeriya sun cancanci amsa kan wannan babakere da sukayi kasa."

Shugaban kasan ya godewa yan kungiyar kwadago da goyon bayan da suke masa da kuma kishin kasar da suka nuna yayin zaben shugaban kasa, musamman bayan dage zabe.

KU KARANTA: Kotun daukaka kara ta yi watsi da shari'ar hana Sani Contact takara

Mun kawo muku cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar kwadagon Najeriya wato NLC karkashin jagorancin shugaban kungiyar ta kasa, Mista Ayuba Wabba, a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, 2019 a fadar shugaban kasa Aso Rock.

Kungiyar kwadagon ta kawowa shugaban kasan gaisuwar taya murna ne kan nasarar da ya samu a zaben ranar 23 ga watan Febraiuru, 2019 inda suka nuna farin cikinsu da yadda Buhari ke gudanar da al'umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel