Jagoran kungiyar matasan Atiku ya sauya sheka zuwa APC, ya sha alwashin mara wa Zulum baya

Jagoran kungiyar matasan Atiku ya sauya sheka zuwa APC, ya sha alwashin mara wa Zulum baya

Jagoran kungiyar kamfen din Atiku Abubakar na matasa a jihar Borno, Hon. Abubakar Saleh Dudu, ya sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC).

Hon. Dudu wanda ya jagoranci sauran kungiyoyin Atiku 35 ya samu tarba daga dan takarar gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum.

Hon. Dudu, wanda ya taba takarar kujerar majalisar dokoki, ya sha alwashin marawa dan takarar gwamnan APC, Zulum baya yayinda ya bukaci mabiyansa da sauran kungioyi da su fito kwanu da kwarkwatansu a ranar Asabar, 9 ga watan Maris domin su zabi APC.

Jagoran kungiyar matasan Atiku ya sauya sheka zuwa APC, ya sha alwashin mara wa Zulum baya
Jagoran kungiyar matasan Atiku ya sauya sheka zuwa APC, ya sha alwashin mara wa Zulum baya
Asali: Twitter

Hon. Dudu ya bayyana cewa akwai dalilai da dama da suka sa shi bari APC sannan ya mara wa Farfesa Zulum baya saboda ya kasance mai mutunci sannan ya kafa tarihi da dama a matsayinsa na malamin jami’a.

KU KARANTA KUMA: Shugaban Majalisa: Matasan Arewa sun mara wa yankin kudu maso kudu baya

A wani lamari na daban, mun ji cewa sama da jam'iyyun siyasa arba'in da ukku ne a jihar Kano suka fito fili suka bayyana goyon bayansu ga dan takarar jam'iyyar APC, Dr Abdullahi Umar Ganduje a ranar Alhamis, domin ba shi damar zarcewa a zaben gwamnoni da za a gudanar a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Yan takarar gwamnnonin karkashin jam'iyyu 43 da suka goyi bayan Gamduje ta bakin mai magana da yawunsu kuma dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar UPC, Ambassador Ibrahim Gaya a wani taron liyafar karin kumallon safe a dakin taro da ke cikin gidan gwamnatin jihar sun bukaci daukacin magoya bayansu da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin zaben APC a ranar Asabar mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel