Jari-hujja: Shugaba Buhari zai sayar da madatsar ruwan Najeriya 6 ga 'yan kasuwa

Jari-hujja: Shugaba Buhari zai sayar da madatsar ruwan Najeriya 6 ga 'yan kasuwa

Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban ta Muhammadu Buhari ta sanar da cewar ta kammala kusan dukkan shirye-shirye domin sayar da madatsan ruwan ta guda shida ga ‘yan kasuwa masu zaman kansu da zummar farfado da su da kuma mayar da shirin ta na BOI.

Wannan dai ya fito ne daga bakin ministan wuta, gidaje da ayyuka Mista Babatunde Fashola wanda ya sanar da hakan da yake jawabi wurin wani taro karo na 29 na masu ruwa da tsaki a fannin wutar lantarki da aka gudanar Minna cikin jahar Neja.

Jari-hujja: Shugaba Buhari zai sayar da madatsar ruwan Najeriya 6 ga 'yan kasuwa
Jari-hujja: Shugaba Buhari zai sayar da madatsar ruwan Najeriya 6 ga 'yan kasuwa
Asali: Facebook

KU KARANTA: EFCC ta damke wani malamin addini dake damfarar mabiyan sa

Legit.ng Hausa ta samu cewa ministan wanda kuma ke zaman tsohon gwamnan jihar Legas ya bayyana cewa, manufar itace don a baiwa cibiyoyin ilimi da ‘yan kasuwa damar dake cikin kasar nan.

Fashola yaci gaba da cewa, wannan duk tsarin gwamnati ne akan kudurin ta na kara samar da wuta a karkara da shugaban kasa ya amince da hakan a 2016.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya da dan takarar shugabancin kasar nan a jam'iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubkar ya bayyana kudurin sa na sayar da matatar man Najeriya watau NNPC, ya sha suka daga talakawan kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel