Asiri ya tonu: Mun gano shirin gwamnatin tarayya na tafka magudi a jihohi 24 - CUPP

Asiri ya tonu: Mun gano shirin gwamnatin tarayya na tafka magudi a jihohi 24 - CUPP

Kungiyar hadakar jam'iyyun siyasa CUPPS ta yi zargin cewa akwai wani shir da gwamnatin tarayya ke yi na ganin cewa APC ta lashe zabe a wasu jihohi 24 a zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki da za a gudanar a ranar Asabar.

Kakakin kungiyar hadakar, Imo Ugochinyere, cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Laraba, ya yi zargin cewa akwai wani shir da gwamnatin tarayya ke yi na ganin cewa APC ta lashe zabe a wasu jihohi 24.

Ya ce, "Daga rahotannin da muka samu, za a cika jihohin Nasarawa, Akwa Ibom, Sokoto, Anambra, Rivers, Taraba, Abia, Gombe da Delta da jami'an tsaron 'yan sanda bayan tayar da tarzoma da nufin taimakawa APC murde zabe da kuma maido jihohin karkashin APC.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Jam'iyyun siyasa 43 sun janye takararsu a Kano, sun goyi bayan Ganduje

Asiri ya tonu: Mun gano shirin gwamnatin tarayya na tafka magudi a jihohi 24 - CUPP
Asiri ya tonu: Mun gano shirin gwamnatin tarayya na tafka magudi a jihohi 24 - CUPP
Asali: Facebook

"Dukkanin jihohin da aka zayyana suna karkashin PDP in banda Nasarawa, wacce ita ma take kokarin kwacewa daga APC."

Ugochinyere ya ce da yawa daga cikin jihohin da aka lissafa a kundin 'yan sanda, wadanda ya hada a cikin sanarwarsa, ba sa fuskantar matsalolin tsaro da har za a ce 'yan sanda su sanya masu idanu.

Ya yi nuni da cewa jihohin Zamfara, Borno da Yobe, wadanda suke fuskantar hare hare da kashe kashe a kowanne lokaci ba su samu karin jami'an tsaro ba.

Ya kara da cewa johohin Kaduna, Katsina da Filato inda ake ci gaba da kashe kashe da garkuwa da mutane tun bayan kammala zaben shugaban kasa ba su samu karin jami'an tsaro ba.

Ya kara da cewa: "Daga bayanan da muka samu, gaba daya sashen rundunar 'yan sanda na MOPOL runduna ta 3 da ke Enugu, da runduna ta 21 da ke FCT da runduna ta 12 da ke Minna, da runduna ta 25 da ke Azumini/Iwukem da kuma runduna ta 45 da ke FHQ Abuja za a mayar da su jihar Nasarawa.

"Rundunar MOPOL ta 22 da ke Ikeje, da ta 49 da ke Epe, da kuma ta 23 da ke FHQ Annex Legas za su koma jihar Sokoto domin taimawa APC ta yi magudi.

"Haka zaika, rundunar MOPOL ta 2 da ke titin Kebbi jihar Legas, da tga 5 da ke Benin, da ta 17 da ke Akure da kuma ta 20 da ke Ikeja, za su koma jihar Akwa Ibom domin taya APC tafka magudi."

Kakakin kungiyar CUPP ya kuma bayyana hanyoyin da gwamnatin tarayyar ta shirya tafka magudin zaben a jihohin da kusan PDP ke shugabanta ko kuma ke da alamar samun nasara a zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokokin da za a gudanar a ranar Lahadi.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel