Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin kungiyar kwadagon Najeriya (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin kungiyar kwadagon Najeriya (Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar kwadagon Najeriya wato NLC karkashin jagorancin shugaban kungiyar ta kasa, Mista Ayuba Wabba, a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, 2019 a fadar shugaban kasa Aso Rock.

Kungiyar kwadagon ta kawowa shugaban kasan gaisuwar taya murna ne kan nasarar da ya samu a zaben ranar 23 ga watan Febraiuru, 2019 inda suka nuna farin cikinsu da yadda Buhari ke gudanar da al'umma.

A jawabin shugaban kungiyar Ayuba Wabba, ya yabawa shugaba Buhari musamman kan kudin fidda kai da ya taimakawa gwamnonin jihohi da shi domin biyan albashin ma'aikata da yan fansho.

Yace: "Dukkanmu bamu manta kudin fidda kai na musamman da ka kaddamar domin taimakawa gwamnatocin jiha ba yayinda kasa ta cika matsin tattalin arziki. Umurnin da ka bada shine gwamnatocin su biya bassusukan albashin da fanshon da ake binsu.

Na tuna kwarai lokacin da ya tambayi gwamnoni shin ta yaya suke iya barci yayinda basu biya ma'aikata albashinsu ba?"

A namu ra'ayin, wannan yana daya daga cikin lokuta mafi jin dadi da muka taba samu da wani shugaban kasar nan.... Ina fada da babban murya cewa wannan ceto da ka kawo ya ceci rayukan ma'aikata da yawa."

A karshe yayi kira ga yan majalisar dokokin tarayya da su hanzarta wajen tafiyar da dokar karin kudin mafi karancin albashi da kuma shugaban kasa ya rattaba hannu.

Kalli hotunan:

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin kungiyar kwadagon Najeriya (Hotuna)
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin kungiyar kwadagon Najeriya (Hotuna)
Asali: Facebook

KU KARANTA: Hotuna: Yadda aka damke dilolin hodar Iblis, muggan kwayoyi, da makamai a jihar Kano

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin kungiyar kwadagon Najeriya (Hotuna)
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin kungiyar kwadagon Najeriya (Hotuna)
Asali: Facebook

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin kungiyar kwadagon Najeriya (Hotuna)
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin kungiyar kwadagon Najeriya (Hotuna)
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel