Kowa ya fita yayi zabe – Buhari ga yan Najeriya

Kowa ya fita yayi zabe – Buhari ga yan Najeriya

Yayin da ake cigaba da zaben Najeriya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga yan Najeriya dasu fita su kada kuri’unsu a yayin zabukan gwamnoni da nay an majalisun jihohi da zai gudana a ranar Asabar, 9 ga watan Maris, a jihohi Talatin na Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne cikin wani sako daya aike ma yan Najeriya a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, inda yace bai kamata ace yan Najeriya sun gagara fita su kada kuri’unsu kawai don an yi zaben shugaban kasa ba.

KU KARANTA: Waka a bakin mai ita: Yadda na kashe mai horas da kungiyarmu– Inji Dan kwallo

“Ina kira gareku daku yi fitan farin dango domin zaben gwamnoninku da yan majalisun jihohinku, ba kawai don an riga an kammala zaben gwamnoni sai mu saki jiki ba, mu ki fitowa zaben gwanoni ba, a’a, zabukan nan masu zuwa suna da matukar muhimmanci kwarai, tamkar na shugaban kasa.

“Hakika jama’a sun fi kusa da masu mulki a jihohinsu, kuma su yafi dacewa su amfanesu kai tsaye, hakan tasa ya zama wajibi mu fita don zaben wadanda zasu shugabancemu a matakin jaha.” Inji shi.

Haka zalika Buhari yayi kira ga jama’a dasu gudanar da zaben cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma su tabbata sun kauce ma duk wasu miyagun halaye kamar su satar akwati, aringizon kuri’u da duk wani aikin da ka iya lalata zaben.

Sa’annan Buhari ya bada tabbacin jami’an tsaro zasu yi iya kokarinsu don ganin sun kare rayukan yan Najeriya tare da dukiyoyinsu, a yayin gudanar da zaben, hakanan zasu sanya idanu don ganin babu wanda ya lalata tsarin zaben.

“A matsayina na dan jam’iyyar APC, ina kira ga yan Najeriya dasu zabi yan takarar jam’iyyar APC daga sama har kasa, watau sak! Domin ina da tabbacin ba zamu baku kunya ba. Mu dage wajen inganta zabukan gwamnoni fiye da na shugaban kasa wanda masu sa ido suka tabbatar da igancinsa.” Inji shi.

Daga karshe Buhari ya jaddada manufarsa ta samar da sahihin zabe a Najeriya, kuma yayi alkawarin cika wannan alkawari don ganin yan Najeriya sun samu damar zaben wanda suka fi cancanta da zasu tuntuda kasar zuwa tudun mun tsira.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel