Zaben gwamna: Jerin jahohi 4 da za'a tafka gumurzu a Arewa

Zaben gwamna: Jerin jahohi 4 da za'a tafka gumurzu a Arewa

A yayin da ake kirga kwanakin da suka rage a kammala gudanar da zabukan shekarar 2019 da zabukan gwamnoni da kuma na 'yan majalisu, kafar labaran ku mai farin jini ta zakulo maku wasu muhimman bayanan yadda zabukan za su iya kasancewa a Arewacin Najeriya.

Kimanin sati biyu da suka gabata dai, yan kasar sun yi fitar kwarin dango inda suka jefa kuri'un su a zabukan shugaban kasa da kuma 'yan majalisar tarayya na Sanatoci da kuma 'yan majalisar wakilai.

Zaben gwamna: Jerin jahohi 4 da za'a tafka gumurzu a Arewa
Zaben gwamna: Jerin jahohi 4 da za'a tafka gumurzu a Arewa
Asali: UGC

KU KARANTA: An kama mutum 18 dake hada-hadar kanun mutane a Najeriya

Legit.ng Hausa ta samu cewa jam'iyya mai mulki a Najeriya ta All Progressives Congress (APC) dai ce ta samu nasara a mafi yawancin jahohin zaben.

A wannan karon kuma ga mu da sharhi kan jahohin da za'a tafka gumurzu a zaben gwamnoni a wasu jahohin Arewacin kasar.

1. Kano:

Za a fafata ne tsakanin gwamna mai ci da ke neman tazarce Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC da kuma dan takarar Kwankwasiyya Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar PDP.

Ana ganin zaben gwamna Kano, fafatawa ce tsakanin tsohon gwamnan jihar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon mataimakinsa gwamna Ganduje wadanda suka yi shekara takwas a gwamnati.

Kawo yanzu kuma, kowa zai iya lashe zaben a cikin 'yan takarar.

2. Sokoto:

Gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal na neman tazarce ne a wa'adi na biyu inda zai yi takara tare da tsohon mataimakinsa Ahmed Aliyu wanda APC ta tsayar dan takararta kuma wanda tsohon gwamnan jihar Aliyu Magatakarda Wamakko ke marawa baya.

Yakin lashe zabe zai kasance ne tsakanin gwamna Tambuwal da ke samun goyon bayan tsohon gwamna Attahiru Bafarawa da kuma Magatakarda Wamakko da ke yakin ganin dan takararsa ya ci zabe.

Ana zaton dai zaben zai yi zafi sosai.

3. Gombe:

Za a fafata ne tsakanin Usman Bayero Nafada na jam'iyyar PDP da kuma dan takarar jam'iyyar APC Inuwa Yahaya

Ana ganin zaben Gombe fafatawa ce tsakanin gwamnan jihar mai barin gado Ibrahim Hassan Dankwambo da kuma tsohon gwamnan jihar kuma uban jam'iyyar APC Danjuma Goje.

Ganin yadda gwamna Dankwambo ya kasa lashe kujerar majalisar dattawa, wasu na ganin babban kalubale ne ga jam'iyyarsa ta PDP da ke mulki a zaben gwamna.

4. Kaduna:

Jihar Kaduna na cikin jihohin da ake ganin zaben gwamna zai ja hankali musamman tsakanin 'yan takarar manyan jam'iyyun siyasa wato APC da kuma PDP.

Gwamnan Kaduna Malam El-Rufai dan takarar APC zai fafata ne da babban mai hamayya da shi Isah Ashiru Kudan na jam'iyyar PDP.

Zaben gwamna a Kaduna zai kara daukar hankali ne ganin yadda gwamna El-Rufa'i ke takun-saka da wasu jiga-jigan jam'iyyarsa ta APC da ya tilastawa sauya sheka zuwa wasu jam'iyyu.

Haka ma kuma ana ganin addini zai yi matukar tasiri a siyasar jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel