Da duminsa: Jam'iyyun siyasa 43 sun janye takararsu a Kano, sun goyi bayan Ganduje

Da duminsa: Jam'iyyun siyasa 43 sun janye takararsu a Kano, sun goyi bayan Ganduje

- Sama da jam'iyyun siyasa arba'in da ukku ne a jihar Kano suka fito fili suka bayyana goyon bayansu ga Dr Abdullahi Umar Ganduje

- Yan takarar ta bakin Ambassador Ibrahim Gayasun bukaci daukacin magoya bayansu da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin zaben APC a ranar Asabar mai zuwa

- Shugaban APC na jihar ya ce Ganduje ya kasance mai kishin demokaradiyya da kuma siyasa ba da gaba ba, wanda kuma ya kasance mai son zaman lafiya

Sama da jam'iyyun siyasa arba'in da ukku ne a jihar Kano suka fito fili suka bayyana goyon bayansu ga dan takarar jam'iyyar APC, Dr Abdullahi Umar Ganduje a ranar Alhamis, domin ba shi damar zarcewa a zaben gwamnoni da za a gudanar a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Yan takarar gwamnnonin karkashin jam'iyyu 43 da suka goyi bayan Gamduje ta bakin mai magana da yawunsu kuma dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar UPC, Ambassador Ibrahim Gaya a wani taron liyafar karin kumallon safe a dakin taro da ke cikin gidan gwamnatin jihar sun bukaci daukacin magoya bayansu da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin zaben APC a ranar Asabar mai zuwa.

Gaya ya ce: "Mun janye takararmu tare da goyon bayan takarar gwamna Ganduje domin ba shi damar kammala ayyukan ci gaba da ya fara a jihar, da nufin bunkasa tattali da walwalar al'ummar jihar."

KARANTA WANNAN: Zaben gwamnoni: Yadda takardun rubuta sakamakon zabe suka bace a Delta

Da duminsa: Jam'iyyun siyasa 43 sun janye takararsu a Kano, sun goyi bayan Ganduje
Da duminsa: Jam'iyyun siyasa 43 sun janye takararsu a Kano, sun goyi bayan Ganduje
Asali: UGC

Da ya ke jawabi a wajen taron, shugaban jam'iyyar APC Alhaji Abdullahi Abbas ya ce gwamnan jihar ne ya shirya taron karin kumallon domin girmama 'yan takarar gwamnan jihar na jam'iyyun da suka janye takararsu, musamman a wannan gabar da ake fuskantar zaben gwamnoni da na 'yan majalisun tarayya.

Ya ce wannan babban ci gaba ne saboda irin hakan bai taba faruwa ba a baya, yana mai cewa: "Ban taba ganin irin wannan lamari ba inda tan takarar gwamna zai gayyaci wasu yan takarar gwamna daga wasu jam'iyyu zuwa yin lifiya tare da shi ba, kuma a cikin mutuntawa."

Ya ce Ganduje ya kasance mai kishin demokaradiyya da kuma siyasa ba da gaba ba, wanda kuma ya kasance mai son zaman lafiya.

A jawabinsa, gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa dalilin gayyatar 'yan takarar gwamnan zuwa gwamnatin jihar shine samar da dai-daito a tsakanin jam'iyyun siyasa a jihar domin kara kauna da dakon zumunci a tsakaninsu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel