Shugaban Majalisa: Matasan Arewa sun mara wa yankin kudu maso kudu baya

Shugaban Majalisa: Matasan Arewa sun mara wa yankin kudu maso kudu baya

Wata kungiyar matasan Arewa a karkashin kungiyar Pan African United Youth Development Network tana son shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress da kuma fadar shugaban kasa da su amince yankin Kudu ta tsayar da shugaban majalisa a majalisar don tabbatar da gaskiya da amfanin kasa.

Kungiyan tace ya kamata mukamin shugaban majalisan dattawa ya koma ga yankin kudu ba don komai ba illa ganin gudumawar da yankin ta bayar wajen cigaban kasar.

Shugaban Majalisa: Matasan Arewa sun mara wa yankin kudu maso kudu baya
Shugaban Majalisa: Matasan Arewa sun mara wa yankin kudu maso kudu baya
Asali: Facebook

Shugaban kungiyan, Habib Mohammed ya fadi hakan ne a wani jawabi da ya gabatar wa jaridar The Nation cewa yankin kudu zata samu wadatacciyar garabasan siyasa idan aka bata ofishin shugaban majalisan dattawa sannan hakan zai tabbatar da ganin ba a samu bangarancin siyasa ba a kasanr.

Kungiyan ta ce: “Ya kamata fadar shugaban kasa da kuma shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) su amince da mika ofishin shugaban majalisa ga yankin Kudu, idan aka yi la’akari da gudumawar yankin ga tattalin arzikin kasa."

KU KARANTA KUMA: Zaben Gwamnoni: Sojin saman Najeriya sun aika jiragen yaki jihohin da za’a iya samun baraka

A wani lamari makamacin haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatinsa ba za su amince masu barna su kasance a mukaman shugabancin majalissun dokokin kasar ba.

Wani babban mataimakin shugaban kasa ne ya bayyana hakan a bisa sharadin ba za a bayyana sunansa ba.

A cewar hadimin, shugaban kasar zai tabbatar da cewa wadanda kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za ta zaba ne kawai zasu riki mukaman shugaban majalisan dattawa da sauran manyan mukamai na majalissun biyu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel