Kwankwaso ne ya rusa ilimi a jihar Kano – Inji Ganduje

Kwankwaso ne ya rusa ilimi a jihar Kano – Inji Ganduje

- Gwamnan jihar Kano Abdullahi Gaduje ya zargi Kwankwaso da rusa ilimi a jihar

- Ganduje ya kuma kalubalanci tsohon gwamnan da ya gabatar da shaaidar kammala karatun injiniya da ya ke ikirarin ya mallaka

- Dan takarar da APC a zaben gwamna mai zuwa ya kara da cewa mai rarraunar kwakwalwa ne kadai zai yi abin da Kwankwaso ke yi wa harkar ilimi a Jihar

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kalubanci tsohon gwamnan jihar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ya gabatar da takardar da ke nuna shaidar cewa ya yi karatun injiniya da ya ke ikirarin ya mallaka.

A cewar Ganduje, Kwankwaso ya sha kaye a jarabawar shiga makarantar gaba da firamare don haka aka tura shi makantar koyon sana’ar hannu. Gwamnan ya kara da cewa dama chan a zamanin baya duk wanda ya fadi jarrabawa shi ake turawa irin wannan makaranta na koyon aikin hannu.

Kwankwaso ne ya rusa ilimi a jihar Kano – Inji Ganduje
Kwankwaso ne ya rusa ilimi a jihar Kano – Inji Ganduje
Asali: Original

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne jiya Laraba, 6 ga watan Maris a lokacin da yake kaddamar da kwamitin biyan kudaden tallafin karatu ga dalibai ‘yan asalin Jihar Kano dake karatu a manyan makarantun kasar.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama dilolin kwaya 54 a Kano

Ganduje ya kara da cewa mai rarraunar kwakwalwa ne kadai zai yi abin da Kwankwaso ke yi wa harkar ilimi a Jihar Kano.

Hakazalika gwamnan ya ce illar da Kwankwaso ya yi wa bangaren ilimi a lokacin da yake mulkin Jihar. “Lokacin muna tare mun ba shi shawarwari akan abin da ya dace a yi wa bangaren ilimi, amma saboda babban abin da ya fi kwarewa shi ne yin watsi da kyawawan shawarwari.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel