Zaben Gwamnoni: Sojin saman Najeriya sun aika jiragen yaki jihohin da za’a iya samun baraka

Zaben Gwamnoni: Sojin saman Najeriya sun aika jiragen yaki jihohin da za’a iya samun baraka

Rundunar sojin saman Najeriya ta turaa jragen yaki zuwa wurare da za a iya samun Baraka domin su taimaka wa sauran hukumomin tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya a lokacin zaben ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Kakakin rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola ya bayyana hakan a wani jawabi da ya saki a Abuja a ranar Laraba, 6 ga watan Maris wanda aka gabatar ga manema labarai.

Daramola ya bayyana cewa Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar ne ya bayyana hakana a lokacin wani taron manyana ma’aikatan rudunar da kuma kwamandoji a hedkwatar ta da ke Abuja.

Zaben Gwamnoni: Sojin saman Najeriya sun aika jiragen yaki jihohin da za’a iya samun baraka
Zaben Gwamnoni: Sojin saman Najeriya sun aika jiragen yaki jihohin da za’a iya samun baraka
Asali: Facebook

Kakakin rundunar yace an yanke wannan shawarar ne daidai da umurnin Shugaban ma’aikatan tsaro Janar Abayomi Olonisakin, wanda ya kuma umurci hukumomin tsaro da su tabbatar da gudanarwar zaben gwamnoni da na yan majalisar jihohi cikin lumana.

A cewarsa an yi wannan shirin ne koda za a samu lamari na karya oda da doka.

KU KARANTA KUMA: Wannan karon masu hana ruwa gudu ba za su karbi ragamar Majalisa - Buhari

Ya umurci kwamadojin sojin sama da na kasa da su tabbatar da zaman lafiya a zaben sannan su kare rayuka da dukiyoyi a lokacin zaben ranar 9 ga watan Maris.

Yace hakki ne da ya rataya a wuyansu kare yan Najeriya da dukiyoyinsu a lokacin zaben.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel