Ka zage damtse wajen neman arzikin man fetur a Arewa - ACF ga Buhari

Ka zage damtse wajen neman arzikin man fetur a Arewa - ACF ga Buhari

Shugaban kwamitin amintattun kungiyar mashawartan Arewa, Malam Adamu Fika, wanda ya jagoranci tawagar mambobin kungiyar zuwa wajen shugaban Buhari domin tayasa murna da kuma janyo hankalinsa kan neman arzikin man fetur a Arewacin Najeriya.

Fika, ya tunawa shugaba Buhari bukatun da suka mika masa a shekarar 2016 na gina tashar ruwar Baro da tashan wutan Mambilla, farfado da bangaren aikin noma, gini da gyaran hanyoyi, da kuma neman arzikin man fetur a Arewacin Najeriya.

Yace: "A shekarar 2016, yayin ziyarar tawagar kungiyar karkashin jagorancin, Marigayi dan masanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule, mun jawo hankalinka kan muradin Arewa da kuma amfanin kasa ga baki daya."

"Ayyukan sun kunshi tashar ruwar Baro, tashan ruwar Mambilla, dogaro da kai wajen aikin noma, gini da gyaran hanyoyi, da kuma uwa uba hakar man fetur da iskar gas."

"Muna farin cikin cewa tun lokacin, an kaddamar da tashar ruwar Baro, yayinda ake cigaba da kokarin aiwatar da sauran ayyuka."

"Muna addu'an cewa ma'aikatun gwamnatin da aka baiwa hakkin aiwatar da aikin su zange damtse wajen ganin cewa sun kammala ayyukan cikin kankanin lokaci."

KU KARANTA: Yan gudun hijra sun shiga addu'a da azumi domin Ndume ya zama shugaban majalisa

Mun kawo muku rahoton cewa tawagar shugabannin kungiyar Arewacin Najeriya ACF sun kaiwa shugaba Muhammadu Buhari ziyarar taya murna kan nasararsa a zaben shugaban kasa.

Kungiyar ACF da daga cikin kungiyoyin da suka marawa shugaba Buhari baya a zaben sabanin kungiyar dattawa Arewa da suka marawa Alhaji Atiku Abubakar baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel