Yan gudun hijra sun shiga addu'a da azumi domin Ndume ya zama shugaban majalisa

Yan gudun hijra sun shiga addu'a da azumi domin Ndume ya zama shugaban majalisa

Kimanin yan sansanin gudun hijra IDP daban-daban a Maiduguri ranar Talata sun fara azumin kwanaki biyar da addu'oi domin Allah ya baiwa Sanata Muhammad Ali Ndume a matsayin shugaban majalisar dattawa.

Yawancinsu da ke sansanin gudun hijran Bakassi; yayinda sauran a wasu sansanin da garuruwan dake cikin Maiduguri.

Babban limanin sansanin gudun hijran Bakassi, Usman Mohammed, yace: "Babu wanda ke daukan nauyinmu domin yin azumi da addu'a. Mun yanke shawaran yin hakan ne da kanmu bisa ga aikin zo a gani da Ndume keyi wajen yaki da Boko Haram."

"Hakazalika gudunmuwan da muka ji yana badawa domin farfado da Arewa maso gabashin Najeriya, musamman rawan da ya taka wajen kafa hukumar arewa maso gabashin Najeriya."

Ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari, gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, da dukkan jiga-jigan APC a jihar Borno da Arewa maso gabas suyi aiki domin nasarar Ndume a matsayin shugaban majalisar dattawa na gaba.

KU KARANTA: Ka zage damtse wajen neman arzikin man fetur a Arewa - ACF ga Buhari

Sanata Ali Ndume ya sake lashe kujerar dan majalisar dattawa mai wakiltan Borno da kudu. Ya fuskanci kalubale da dama a majalisar karkashin jagorancin Bukola Saraki inda aka tsigesa daga kujerar shugaban masu rinjaye.

Daga baya kuma aka dakatad da shi na tsawon watanni shida don bayyana ra'ayinsa ga jama'a kan abubuwa da ke faruwa a majalisa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel