Zabe: Cancanta za a bi ba sak ba – Aisha Buhari

Zabe: Cancanta za a bi ba sak ba – Aisha Buhari

- Alamu sun nuna akwai yan kananan rikice-rikice a jam’iyyar APC a jihar Adamawa

- Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha ta bayyana cewa cancanta za’a yi a jihar Adamawa ba wai “SAK” ba

- Aisha Buhari ta godewa Al’umma tare da yaba musu bisa nasarar da maigidanta ya samu a zaben da ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu

A daidai lokacin da zaben gwamnoni da na yan majalisar dokokin jihohi ke kara gabatowa, alamu sun nuna akwai yan kananan rikice-rikice a jam’iyyar APC a jihar Adamawa.

A karon farko Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha ta yi tsokaci a kan batun siyasar jihar Adamawa, inda ta bayyana cewa cancanta za’a yi a jihar ba wai “SAK” ba.

Zabe: Cancanta za a bi ba sak ba – Aisha Buhari
Zabe: Cancanta za a bi ba sak ba – Aisha Buhari
Asali: Getty Images

Tun daga lokacin da jam’iyyar APC mai mulki a jihar ta sha kasa a zaben Shugaban kasa a jihar, aka fara yamutsa gashin baki da zarge-zarge a tsakanin manyan jam’iyyar.

Aisha Buhari ta godewa Al’umma tare da yaba musu bisa nasarar da maigidanta ya samu a zaben da ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu, sannan ta ce dole ne jama’a su tantance wadanda za su zaba a wannan karon ba wai su yi zaben “SAK” ba.

KU KARANTA KUMA: Wannan karon masu hana ruwa gudu ba za su karbi ragamar Majalisa - Buhari

Amma a martanin da jam’iyyar APC ta mayar ta hannun sakataran tsare -tsaren jam’iyyar a jihar Adamawa, Ahmed Lawal, ta ce ba za su lamuncewa wadanda ke yi wa jam’iyyar zagon kasa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel