'Yan Kudu maso Kudu sun gabatar da muhimmiyar bukata a majalisar tarayya

'Yan Kudu maso Kudu sun gabatar da muhimmiyar bukata a majalisar tarayya

Shugabanin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na yankin Kudu maso Kudancin Najeriya sun nemi a basu mukammin shugaban majalisar dattawa na kasa.

Sun mika wannan bukatan ne cikin sakon taya murna da suka aike wa Shugaba Muhammadu Buhari a kan nasarar da ya samu na lashe zaben shugban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.

A sakon da suka fitar a ranar Laraba, mataimakin shugaban jam'iyyar APC na Kudu maso Kudu, Ntufam Etta ya ce yankin ta cancanci a bata wannan matsayin.

'Yan Kudu maso Kudu mun gabatar da muhimmiyar bukata a majalisar tarayya
'Yan Kudu maso Kudu mun gabatar da muhimmiyar bukata a majalisar tarayya
Asali: Facebook

Ya ce, "Yankin mu ta dade tana bayar da gudun mawa domin ganin kasar mu ta cigaba kuma za mu cigaba da yin hakan.

DUBA WANNAN: Al'ajabi: 'Yan Najeriya 5 da ke ikirarin sun mutu, sun shiga aljannan sun dawo

"Shugabanin jam'iyyar mu sun taka muhimmiyar rawa wurin tabbatar da zaman lafiya a yankin domin ganin kasuwancin ta cigaba da kuma wayar da kan matasan mu kan muhimmancin zaman lafiya.

"Muna mika godiyar mu ga dukkan shugbanin yankin da matasa bisa goyon bayan da suka bawa shugbaban kasa domin ya cigaba a ayyukan cigaba. Zamanin da matasan mu ke tayar da kayan baya domin hana cigaba ya wuce."

Ya kara da cewa, "Mun tuna cewa dan mu Sanata Joseph Wayas ya rike mukamin shugaban majalisar dattawa kuma ya taka rawar gani. A karkashin shugabancin sa, fadar shugaban kasa da majalisa da sashin shari'a sunyi aiki cikin lumana domin cigaba 'yan Najeriya.

"Saboda haka, zaben shugaban majalisa daga Kudu maso Kudu zai daidaita siyasar kasar nan domin majalisa ta mayar da hankali a kan tsara dokoki. Kazalika, zaben shugaban majalisa daga yankin mu zai hana afkuwar matsala a cikin fadar shugaban kasa kamar yadda muka gani a baya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel