Zidane ya fadawa Real Madrid bai da sha’awar dawowa Kulob din

Zidane ya fadawa Real Madrid bai da sha’awar dawowa Kulob din

Kungiyar Real Madrid sun fara kokarin dawo da tsohon kocin su watau Zinedine Zidane domin ya dawo ya gyara halin da ake ciki a kulob din ganin yadda abubuwa su ka sukurkuce mata a halin yanzu.

Kamar yadda mu ke samun labari, Real Madrid ta na neman taya Zinedine Zidane wanda shi kuma ya nuna sha’awar bai da niyyar komawa kungiyar da ya bari. Gidan labarai na sportbible.com su ka rahoto wannan a makon nan.

A cikin makon nan ne aka fatattaki Real Madrid daga gasar karamin kofin gida watau Copa Del Rey, da La-liga na kasar Sifen, sannan kuma aka yi waje da su daga gasar zakarun cin kofin Nahiyar Turai a hannun FC Ajax.

KU KARANTA: Yadda na kashe Kocin kungiyar mu– Inji wani 'Dan wasa

Zidane ya fadawa Real Madrid bai da sha’awar dawowa Kulob din
Zidane ya fadawa Shugaban Real Madrid bai da shirin dawowa
Asali: Getty Images

Rahotanni sun bayyana mana cewa shugaban kungiyar Real, Florentino Perez ya kira Zidane a wayar salula domin ya dawo ya cigaba da horas da kulob din. Zidane kuma ya bayyanawa Perez cewa bai da sha’awar dawowa Madrid.

Tsohon shugaban kulob din na Sifen, Ramon Calderon, shi ne ya fasa kwan cewa Real Madrid na neman Zidane ya taimaka ya dawo. Calderon yace Zidane ya nuna cewa akwai yiwuwar ya dawo kulob din amma a karshen kakar bana.

Koci Zidane dai ya bar kungiyar da ya bugawa wasa a karshen rayuwar sa ne bayan ya sake lashe kofin Turai. Kocin ya bar kulob din ne a lokacin da babban ‘dan wasan da ta ke ji da shi watau Cristiano Ronaldo ya tashi ya koma Juventus.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel