Jam’iyyyu 35 sun hada kai a Kwara, sun mara wa dan takaran APC baya

Jam’iyyyu 35 sun hada kai a Kwara, sun mara wa dan takaran APC baya

- Gabannin zaben gwamnoni da na yan majalisar jihohi da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa, akalla jam’iyyun siyasa 35 ne suka hada kai da APC

- Sun tsayar da dan takarar gwamnan jam'iyyar APC a matsayin zabinsu a zaben

- A cewar jam'iyyun suna burin ganin jihar Kwara ta samu ci gaban da take muradi ne

Gabannin zaben gwamnoni da na yan majalisar jihohi da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa, akalla jam’iyyun siyasa 35 ne suka hada kai a karkashin Kwara Like-minds Political Parties (KLPP), inda suka jone da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sannan kuma suka tsayar da dan takaranta na gwamna, Abdulrahman Abdulrazaq.

Jam’iyyun sun hada da, Peoples Party of Nigeria (PPN); African Democratic Party of Nigeria (ADPN); National Conscience Party (NCP); National Conscience Party of Nigeria (NCPN); People for Democratic Change (PDC); Change Advocacy Party of Nigeria (CAPN); Peoples Trust (PT), da kuma National Democratic Liberty Party (NDLP).

Jam’iyyyu 35 sun hada kai a Kwara, sun mara wa dan takaran APC baya
Jam’iyyyu 35 sun hada kai a Kwara, sun mara wa dan takaran APC baya
Asali: Depositphotos

Wannan lamarin ya baiwa jam’iyyar APC damar kyautata zatton cewa ita ce za ta lashe zaben da za a gudanar a ranar 9 ga watan Maris a jihar.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dokokin Adamawa ta rasa dan majalisa karo na biyu a cikin mako guda

A baya, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Bashir Bokarinwa, ya nuna wa kungiyar godiyarsa da ta hada dangantaka da APC a jihar a yunkurinta na yanta mutanen jihar Kwara, inda yake cewa babu shakkan cewa wannan hadewar da jam’iyyu suka yi na bukatar masu ruwa da tsaki da kungiyoyi da su fito bainar jama’a don mara wa jam’iyyar gabannin zaben 9 ga watan Maris a jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel