Wannan karon masu hana ruwa gudu ba za su karbi ragamar Majalisa - Buhari

Wannan karon masu hana ruwa gudu ba za su karbi ragamar Majalisa - Buhari

- An rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna ra'ayi akan wanda zai zamo shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai

- Sai dai kuma shugaban kasar bai da wanda yake so su hau kan kujerun

- Wani hadimin shugaban kasa yace Buhari ba zai bari rashin bin doka da ya afku a 2015 ya sake maimaita kansa ba

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatinsa ba za su amince masu barna su kasance a mukaman shugabancin majalissun dokokin kasar ba.

Wani babban mataimakin shugaban kasa ne ya bayyana hakan a bisa sharadin ba za a bayyana sunansa ba.

A cewar hadimin, shugaban kasar zai tabbatar da cewa wadanda kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za ta zaba ne kawai zasu riki mukaman shugaban majalisan dattawa da sauran manyan mukamai na majalissun biyu.

Wannan karon masu hana ruwa gudu ba za su karbi ragamar Majalisa - Buhari
Wannan karon masu hana ruwa gudu ba za su karbi ragamar Majalisa - Buhari
Asali: UGC

Yace fadar shugaban kasar bata taba samun tsanaki ba a dangantaka tsakaninta da shuwagabannin majalissun, saboda haka, ba za ta zauna ta kalli wassu marasa faraha su dauki hakkin shugabanci ba a karo mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyyu 35 sun hada kai a Kwara, sun mara wa dan takaran APC baya

Daga farkon Majalissun, shugaban majalisan dattawa Bukola Saraki da kakakin majalisan wakilai Yakubu Dogara, sun lashe mukaman ne, ba a bisa tsarin da shugabancin APC ta shirya ba.

A halin da ake ciki, gaabannin zaben gwamnoni da na yan majalisar jiha, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jawabi ga yan Najeriya inda yayi kira ga su rungumi zaman lafiya a tsarin gudanarwar zaben.

A jawabin da yayi a ranar Laraba, 6 ga watan Maris, Shugaban kasar ya bayyana cewa zabe mai zuwa na da matukar muhimmanci duba ga cewa gwaamnoni da yan majalisar jiha sun fi kusa da mutane sosai.

Shugaba Buhari ya mika ta’aziyya ga wadanda suka rasa rayukansu ko suka ji rauni da lokacin ayukan ta’addanci da wasu suka yi yayin zaben Shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel