Gwamnatin tarayya ta yi tirr da kasar Kamaru bisa koro 'yan gudun hijirar Nijeriya 40,000

Gwamnatin tarayya ta yi tirr da kasar Kamaru bisa koro 'yan gudun hijirar Nijeriya 40,000

-Kasar Kamaru ta tasa keyar 'yan gudun hijirar Nijeriya 40,000 gida

-Kamaru ta saba ka'idojin majalisar dinkin duniya na mutunta 'yan gudun hijira

-Gwamnatin Nijeriya ta roki kasar Kamaru da kar ta koro 'yan gudun hijiran, amma Kamaru ta yi kunnen uwar shegu

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi Allah wadai da dawo da 'yan Nijeriya dubu arba'in da kasar Kamaru ta yi, da ke zaman 'yan gudun hijirar da yakin Boko Haram ya kora daga matsugunansu a yankin karamar hukumar Rann.

Gwamnatin Nijeriya ta ce sai da ta roki alfarmar kasar Kamaru da kar ta dawo da 'ya'yanta da ke gudun hijira sakamakon raba sy da matsugunansu da Boko Hama ta yi a Rann.

Shugabar hukumar lura da 'yan gudun hijara, Sadiya Farouq ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata a Abuja.

KU KARANTA: Dan majalisar Dokokin jihar Adamawa ya rasu kwanaki uku kafin zabe

Ta ci gaba da cewa sai da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta nemi alfarma a wajen takwararta ta kasar Kamaru da kar ta kori 'yan gudun hijirar a lokacin da ta yi barazanar korar su a baya.

Sadiya Farouq ta ci gaba da cewa, gwamnatin tarayya ta ofishin ma'aikatar harkokin waje za ta dauki matakan da ya dace a kan wannan batu.

"Abin takaici ne matuka, duk da rokon da gwamnatin tarayya ta yi ga gwamnatin Kamaru da kar ta kori 'yan Nijeriya da yakin Boko Haram ya kora daga matsugunansu a karamar hukuma Rann, jihar Borno, amma wannan roko ya kasa samun karbuwa a kunnen gwamnatin Kamaru."

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kama dilolin kwaya 54 a Kano

"Labarin da ke ishemu shi ne na cewa wai gwamnatin Kamaru ta fatattaki mutanenmu da suka yi gudun tsira da rai kuma suka kafa sansani a yankin kasar Kamarun. Wannan lamari ko shakka babu ya saba da ka'idojojin kare 'yan gudun hijira na majalisar dinkin duniya da kasashen biyu suka sanya wa hannu."

"Tsarin dokar majalisar dinkin duniya da kasashe 167 na duniya suka sanya wa hannu ya ce, 'Babu wata kasa da za ta dawo da, ko ta kori wani dan gudun hijira ya koma zuwa kasarsa ba musamman inda rayuwarsa ko 'yancinsa ke cikin hatsari kuma ko mene ne addini, launi kasar da ya fito ko akidarsa ba," inji sanarwar.

KU KARANTA: Dan wasa ya halaka kocinsa a jihar Kano

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel