Yan sanda sun kama dilolin kwaya 54 a Kano

Yan sanda sun kama dilolin kwaya 54 a Kano

Rundunan yan sanda reshen Jihar Kano ta tabbatar da kamun masu safaran miyagun kwayoyi cikin babban birnin jihar.

Kakakin rundunar yan sanda a jihar, DSP Abullahi Haruna wanda ya tabbatar da kamun a jawabin da ya gabatar wa manema labarai a Kano a ranar Laraba ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargi da laifin safararsu a lokacin da rundunar ke gudanar da ayyuka na musamman a jihar.

Yace wassu daga cikin wadanda ake zargin sun kasance da hannu a safaran hodar iblis, tabar wiwi, shaka ka mutu, tramadol da sauran miyagun kwayoyi.

Haruna yace an kama wani mai suna Mujahid Abubakar da Iliya Garba a kasuwar Sabon Gari inda aka gano kwayoyi masu dunbin yawa.

Yan sanda sun kama dilolin kwaya 54 a Kano
Yan sanda sun kama dilolin kwaya 54 a Kano
Asali: Depositphotos

Jerin kwayoyin da aka gano sun hada da: Tablet Exol 5 -39000 tabs, Tablet Sycozines 5 – 21000 tabs, Injection Diazepam – 166000 Bottles, Injection Tranzile -7000 Bottles, Injection Tramadol – 2150, Injection Ejon Merinetin – 8000, Injection Nart phenobartil – 180, Injection penzozine – 40, Injection Voltean – 14, C0cadamol Tablet – 1600.

Yace wadanda ake zargin sun amsa laifin yayin da ake cigaba da karfafa ayyuka don kama sauran masu hannu cikin mugun aikin.

A wani lamari mai kama da haka, kakakin rundunar ya tabbatar da kama wani Muhammed Abdullahi babban dan safaran hodar iblis.

KU KARANTA KUMA: Waka a bakin mai ita: Yadda na kashe mai horas da kungiyarmu– Inji Dan kwallo

Yace mai laifin ya kasance mazaunin Hotoro Quarters kuma an kama shi a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2019.

Kakakin rundunan yace mai laifin a halin yanzu yana ba yan sanda hadin kai a binciken da take gudanarwa kafin gurfana a kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel