2019: Fasto Julius Ediwe ya nemi Jama’a su sa Shugaba Buhari a addu’a

2019: Fasto Julius Ediwe ya nemi Jama’a su sa Shugaba Buhari a addu’a

Wani Limamin addinin Kirista, Bishof Julius Ediwe, ya fito ya bayyana cewa Ubangiji ne ya ba shugaban kasa Muhammadu Buhari sa’a a zaben da aka yi kwanan nan inda ya samu damar zarcewa kan mulki.

Wannan fasto da yake jawabi a da ke babban birnin tarayya yace tun kwanakin baya Malamai su ka gane cewa Buhari ne zai ci zaben na bana a lokacin da su kayi kwanaki 40 su na faman yin sallah da azumi a kan zaben shugaban kasa.

Jagoran Fastocin yankin Kudu maso kudancin kasar, Bishof J. Ediwe yana cikin wadanda su ke ganin cewa shugaba Buhari ba zai sha kasa a zaben na Najeriya ba. Tun wancan lokaci ya rika sukar ‘yan uwan sa masu akasain wannan ra’ayi.

KU KARANTA: Buhari ya gana da wasu Dattawan Arewa a fadar Aso Villa jiya

2019: Fasto Julius Ediwe ya nemi Jama’a su sa Shugaba Buhari a addu’a
Nasarar Buhari daga Allah ne don haka sai dai ayi masa addu’a inji Julius Ediwe
Asali: UGC

Julius Ediwe yayi wannan bayani ne a wajen wani biki da Malaman addini daban-daban su ka shirya domin murnar nasarar da shugaba Buhari ya samu. An yi wannan biki ne a farfajiyar Unity Fountain da ke cikin babban birnin tarayya Abuja.

Limamin na kirista ya kawo ayoyi daga cikin sura ta biyu a Al-Qur’ani watau Surah Al-Baqara, a ya ta 153 inda Ubangiji ya nemi Bayin sa da su zama masu hakuri, sannan kuma su rika yawan addu’a domin su kasance tare da rahamar Allah.

Bisa wannan ne Malamin na addinin kirista ya jawo hankalin ‘yan uwan Shehunan Malaman addini da su ajiye duk banbancin da su ke da shi a gefe guda, su yi wa kasa addu’a. Malamin yace tun tuni dai ya san cewa APC ce za ta ci zaben bana.

Faston ya kuma soki masu cewa an murde zaben na shugaban kasa a wasu yankunan Kudancin Najeriya. Ediwe yace a matsayin sa na Limamin da ya fito daga Kudu bai yarda da wannan zance ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel