Mutum 1 ya mutu yayin da matasan APC dana PDP suka yi arangama a Kaduna (Hotuna)

Mutum 1 ya mutu yayin da matasan APC dana PDP suka yi arangama a Kaduna (Hotuna)

Akalla mutum daya ne ya rasa ransa yayin da matasan jam’iyyun hamayya na APC da na PDP suka yi arangama a cikin garin Kaduna, inda suka jikkata juna tare da barnata dukiyoyin jama’a da basu ji ba, basu gani ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito anyi wannan karan batta ne a ranar Laraba, 6 ga watan Maris a unguwar Kurmin Gwari dake cikin karamar hukumar Kaduna ta kudu, inda gungun matasan biyu suka fita yakin neman zabe.

KU KARANTA: Zan rungumi kaddara idan har aka kayar dani a zabe – Gwamna Ganduje

Mutum 1 ya mutu yayin da matasan APC dana PDP suka yi arangama a Kaduna (Hotuna)
Mutum 1 ya mutu yayin da matasan APC dana PDP suka yi arangama a Kaduna
Asali: Facebook

Matasan jam’iyyar APC sun fita ne da nufin taya gwaninsu dake takarar kujerar dan majalisar dokokin jahar Kaduna yakin neman zabe, haka zalika suma matasan PDP sun fita ne da nufin taya nasu gwanin dake neman wannan kujera yakin neman zabe.

Ana cikin haka ne sai suka yi kicibus da juna a Kurmin Gwari da Kakuri, ba tare da bata lokaci ba dukkaninsu suka zaro makamai, suka afka ma juna, sa’annan suka shiga farfasa gilasan duk wata motar da suka gani a wajen, tare da fasa tayoyinta da kuma afka ma shagunan jama’a.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar, ASP Nafiu Habib ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace tuni rundunar ta aika da jami’anta don tabbatar da zaman lafiya a yankin, tare da kwantar da hankulan jama’an dake yankin.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa shi zai fara kiran duk wanda ya lashe zaben da kansa don tayashi murna, idan har zaben ya kasance na gaskiya da gaskiya ne, kuma zai rungumi kaddara, tare da sanin cewa Allah ne ke yi.

Gandujen ya bayyana haka ne bayan rattafa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da yan takararar gwamnna jahar Kano suka yi karo na biyu a karkashin jagorancin kwamitin zaman lafiya ta jahar Kano a ranar Laraba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel