Innalillahi wa inna Ilaihi raji’un: Mahaifiyar Sheikh Daurawa ta rasu

Innalillahi wa inna Ilaihi raji’un: Mahaifiyar Sheikh Daurawa ta rasu

Shahararren malamin addinin nan, kuma shugaban hukumar Hisbah ta jahar Kano, Sheikh Aminu Daurawa, ya yi rashin mahaifiyarsa, kamar yadda Shehin Malamin ya bayyana da kansa.

Legit.ng ta ruwaito Daurawa ya bayyana haka ne a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda yace za’a gudanar da jana’izar mahaifiyar tasa ne a gidansa dake unguwar Yar Akwa, cikin garin Kano.

KU KARANTA: Zan rungumi kaddara idan har aka kayar dani a zabe – Gwamna Ganduje

“Inna lillah wa inna ilaihi rajiun Allah ya yiwa Hajiya babata rasuwa zaayi Janaiza a gidana na Unguwar yar akwa kusa da Darussunnah ko makarantar zam zam da misalin karfe sha daya na safe inshaa Allahu” Inji shi.

Innalillahi wa inna Ilaihi raji’un: Mahaifiyar Sheikh Daurawa ta rasu
Daurawa da mahaifiyarsa
Asali: Facebook

Idan za’a tuna a kwanakin baya ne dai Daurawa ya jagoranci Malamai da Limamai dari zuwa gidan jagoran darikar siyasa ta Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a daidai lokacin da ake tsaka da nuna ma juna yatsa tsakanin Kwankwaso da wasu Malaman kungiyar Izala.

Sai dai Daurawa ya bayyana cewa dalilin zuwansa gidan Kwankwaso shine don samar da sulhu tsakanin Kwankwaso da mabiyansa a bangare guda, da kuma Malaman a bangare guda, bayan samun rahoton kowanne bangare ya wasa wukarsa don karo da juna.

“Mun samu labarin Malamai sun shirya gudanar da huduba akan Kwankwaso, haka zalika wasu magoya bayan Kwankwaso sun dauki alwashin cin mutuncin duk Malamin daya soki gwaninsu, don haka muka shiga tsakani don ganin cewa Kwankwaso ya taushi mabiyansa, kuma an samu nasara.” Inji shi.

A wani labarin kuma, wasu rahotanni sun yi nuni da cewa gwamnatin jahar Kano ta garkame ofishin Daurawa dake babban sakatariyan hukumar Hisbah ta jahar Kano, sai dai da aka tambayi Malamin, sai yace bashi da labari game da hakan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel