Alkali ta tsige mai neman kujerar Majalisar Dokoki a APC a Jihar Edo

Alkali ta tsige mai neman kujerar Majalisar Dokoki a APC a Jihar Edo

Babban kotun tarayya da ke cikin garin Benin a jihar Edo, tayi wani zama jiya Laraba inda ta soke takarar Osaro Obaze mai neman kujerar majalisar dokoki na yankin Oredo a karkashin jam’iyyar APC.

Babbar Alkali mai shari’a a Benin, Damilola Ajayi, ta bada wani sabon hukunci cewa Mista Ekhosuehi Aiguobahi shi ne ainihin ‘dan takarar jam’iyyar APC mai mulki a a zaben majalisar dokokin jihar da za ayi Ranar Asabar dinnan.

Alkalin ta maye gurbin Osaro Obaze, wanda ake tunani cewa shi ne zai rikewa APC tuta a zaben da za ayi da Ekhosuehi Aiguobahi wanda ya kai kara kotu. Ekhosuehi Aiguobahi yana ikirarin cewa shi ne ya ci zaben fitar da gwani.

KU KARANTA: Zan rungumi kaddara idan har na sha kasa a zaben 2019 – Ganduje

Alkali ta tsige mai neman kujerar Majalisar Dokoki a APC a Jihar Edo
Kotu ta canza 'Dan takarar APC na Majalisa a Yankin Oredo
Asali: Depositphotos

Kwanaki ne Aiguobahi ya maka jam’iyyar sa da ‘dan takarar da aka tsaida a gaban Alkali yana nema kotu ta dakatar da wancan abokin hamayyar ta sa, ta tsaida sa a matsayin ‘dan takara. Yanzu kotu ta amince da wannan roko na sa.

Kotu tace Ekhosuehi shi ne wanda ya lashe zaben tsaida ‘dan takara na jam’iyyar APC da aka yi kwanakin baya, don haka tace shi zai tsaya takara a babban zaben da za ayi a karshen makon nan yayin da Osaro Obazee yace bai yarda ba.

Osaro Obaze har yanzu yana da’awar cewa shi ne ‘dan takarar APC ba kowa ba domin sunan sa na gaban hukumar zabe na INEC. Obaze dai ya so ne ya nemi kujerar majalisar tarayya na yankin Oredo ne a zaben 2019 amma ya hakura.

Jam’iyya dai tace har yanzu Hon. Osaro Obaze shi ne asalin ‘dan takarar ta a yankin Oredo ta gabas a zaben da za ayi. ‘Dan takarar ya hakikance a kan cewa shi ne wanda ya ci zabe ba E. Aiguobahi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel