An sake kwatawa: Yan bindiga sun bindige mutane 30 a jahar Zamfara

An sake kwatawa: Yan bindiga sun bindige mutane 30 a jahar Zamfara

Har yanzu yan bindiga na cigaba da cin karensu babu babbaka a yankuna daban daban na jahar Zamfara, inda suke kashe jama’a babu gaira babu dalili, suna yin garkuwa da wasu, tare da lalata musu dukiya, haka nan siddan ba tare da wani dalili ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Talata, 5 ga watan Maris ma wasu gungun yan bindigan sun kaddamar da hare hare a kauyen kware dake cikin lardin Shinkafi ta jahar, inda suka kashe akalla mutane 30, bayan sun bude musu wuta tare da kona gidajensu.

KU KARANTA: Zaben gwamna: Malaman makarantun Kaduna sun jaddada goyon baya ga El-Rufai

Wani mazaunin kauyen, Alu Wadata ya bayyana cewa sun gano gawarwakin mutane 34; “Mun gano gawarwakin mutane 34 bayan yan bindigan sun wuce, kuma har yanzu akwai mutanen da bamu san halin da suke ciki ba.

“Da misalin karfe 4 na rana suka shigo kauyen, inda suka bude mana wuta babu kakkautawa, suna harbin duk wanda suka gani, tare da kona gidajen jama’a.” Inji shi.

Sai dai mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Zamfara, Mohammed Shehu ya bayyana cewa “Ina tabbatar muku da cewa yan bindiga sun kashe mutane 30 a kauyen Kware.”

Wannan hari dai ya zo ne bayan kwanaki uku da yan bindiga suka kai kwatankwacin harin nan a kauyen Kware, inda suka kashe yan kato da gora guda 32 a wani shingen binciken ababen hawa.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Kaduna ta tabbatar da wani mummunan hari da wasu gungun yan bindiga da ba’a san daga inda suka fito ba suka kai kauyen Sabon Sara na cikin karamar hukumar Giwa ta jahar Kaduna.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar, DSP Yakubu Sabo ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Lahadi, 3 ga watan Feburairu, inda yace maharan sun kashe mutane biyar, sun jikkata wasu mutum goma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel