Zan rungumi kaddara idan har aka kayar dani a zabe – Gwamna Ganduje

Zan rungumi kaddara idan har aka kayar dani a zabe – Gwamna Ganduje

A yayin da zabukan gwamnonin Najeriya ya rage saura yan kwanaki kalilan da basu wuce kwanaki biyu ba, gwamnan jahar Kano, kuma dan takarar gwamna a inuwar jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana burinsa na rungumar kaddara idan har ya sha kayi a zaben.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ganduje ya bayyana cewa shi zai fara kiran duk wanda ya lashe zaben da kansa don tayashi murna, idan har zaben ya kasance na gaskiya da gaskiya ne, kuma zai rungumi kaddara, tare da sanin cewa Allah ne ke yi.

KU KARANTA: Sunayen yan siyasa 18 dake muradin darewa kujerar gwamnan jahar Borno

Zan rungumi kaddara idan har aka kayar dani a zabe – Gwamna Ganduje
Yayin rattafa hannu
Asali: Twitter

Gandujen ya bayyana haka ne bayan rattafa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da yan takararar gwamnna jahar Kano suka yi karo na biyu a karkashin jagorancin kwamitin zaman lafiya ta jahar Kano a ranar Laraba.

“Hakika a shirye nake na amince da sakamakon zabe, saboda hakan shine abinda Allah Ya tsara, kuma ni mutum ne daya amince da duk abinda Allah Ya tsara, idan wani da ba ni ba ya lashe zaben, tabbas zan rungumi kaddara, kuma zan kirashi na tayashi murna.” Inji shi.

Yan takarar kujerar gwamnan Kano su 31 daga jam’iyyu daban daban ne suka halarci taron, suka kuma rattafa hannu akan yarjejeniyar zaman lafiyan, daga ciki har yan takara mata guda 9, manufar yarjejeniyar shine neman goyon bayansu ta yadda za’a gudanar da zaben gwamnoni da nay an majalisun dokokin jaha cikin kwanciyar hankali.

Idan za’a tuna, kimanin yan takarar gwamna guda 30 ne suka rattafa hannu akan irin wannan yarjejeniya a watan data gabata kafin gudanar da zaben shugaban kasa dana yan majalisun tarayya.

Sai dai shugaban kwamitin zaman lafiya na jahar Kano, Rabaran John Namaza Niyiring ya bayyana cewa sun fahimci akwai bukatar rattafa hannu akan yarjejeniya na biyu ne sakamakon tashin tashinan da aka samu a wuraren yakin neman zabe, musamman ma a Dwakin Tofa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel