Gwamnan Kaduna ya karyata rade-radin shirin sake korar Ma’aikata

Gwamnan Kaduna ya karyata rade-radin shirin sake korar Ma’aikata

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya fito yayi bayani game da jita-jitar da ake ji na cewa yana niyyar sallamar wasu ma’aikatan gwamnati daga aiki. Gwamnan yace babu gaskiya a maganar.

Gwamnan Kaduna ya karyata rade-radin shirin sake korar Ma’aikata
El-Rufai yace wannan yakardar da ke yawo ba daga hannun Gwamna ta fito ba
Asali: Facebook

Mai girma Malam Nasir El-Rufa’i, yayi wannan jawabi ne a Ranar Talata bayan wata takarda ta fara yawo inda aka fahimci cewa ya umarci shugaban ma’aikatan gwamnati da ya kori wasu ma’aikata kamar yadda aka yi a baya.

Gwamnan yake cewa sharrin ‘yan adawa ne kurum wadanda su ka hango cewa sun sha kasa tun kafin a kai ko ina, Nasir El-Rufa’i ta bakin babban Hadimin sa, Mista Samuel Aruwan, yace sam wannan takarda ba ta fito daga ofishin sa ba.

KU KARANTA: Jam’iyyun 45 sun cin ma matsaya game da sabon Gwamnan Gombe

A takardar an ji gwamnan yana bada umarni a sallami duk ma’aikacin da ya haura shekara 50 daga aiki, sannan kuma ayi wa wadanda su ka kai mataki na koli a gwamnati ritaya da karfi da yaji. Haka kuma za a ragewa wasu matsayi.

Mai girma Gwamnan yace wannan takarda da ake gani tana yawo da sunan ta fito daga hannun babban Sakataren sa na musamman watau Salisu Sulaiman, ta jabu ce wanda ba gaskiya ba. Gwamna yake cewa aikin ‘yan adawa ne.

Gwamnan wanda ya kori dubban ma’aikatan makaranta da na kananan hukumomi da sauran su a jihar Kaduna, ya dai tabbatar da cewa wannan karo bai da wannan niyya a zuciya na kuma koran wasu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel