Jihohi 7 da ba za a yi zaben gwamna ba ranar Asabar

Jihohi 7 da ba za a yi zaben gwamna ba ranar Asabar

- A ranar Asabar, 9 ga watan Maris, ne ‘yan Najeriya za su kara koma w mazabun su domin zaben gwamnoni da mambobin majalisar dokokin jihohi

- Sai dai zaben, musamman na kujerar gwamna, ba a dukkan jihohin kasar nan za a yi shi ba

- Za a tsallake wasu jihohi 7 da a baya dalilai daban-daban su ka jawo aka gudanar da zabukan su a wasu lokuta mabanbanta

A ranar Asabar, 9 ga watan Maris, ne ‘yan Najeriya za su kara koma wa mazabun su domin zabar gwamnoni da mambobin majalisar dokoki da za su jibinci al’amuran mulki a matakin jiha na tsawon shekaru hudu (zangon mulkin guda).

Sai dai ba a dukkan jihohin Najeriya za a yi zaben gwamna ba a ranar Asabar mai zuwa, za tsallake wasu jihohi bakwai sai daga baya.

Jihohin bakwai su ne; Osun, Ekiti, Edo, Ondo, Anambra, Bayelsa da Kogi. Za a gudanar da zaben gwamna a wadannan jihohi a lokuta mabanbanta.

Jihohi 7 da ba za a yi zaben gwamna ba ranar Asabar
Buhari a wurin zabe
Asali: UGC

Zabuka a wadannan jihohi sun banbanta da ragowar ne saboda hukuncin kotuna na soke zabe ko karba daga hannun wata jam’iyyar a bawa wata.

Mai yiwuwa PDP ta kwashi garabasa a jihar Ribas bayan kotu ta haramta wa hukumar zabe ta kasa (INEC) karbar sunayen ‘yan takara daga hannun jam’iyyar APC a jihar.

DUBA WANNAN: Ban mutu ba, ina nan da rai da lafiya ta – Matashin da ya yi iyo a kwata saboda Buhari

A yayin wani taro da magoya bayan APC a jihar Ribas, jagoran jam’iyyar a jihar Ribas da ma yankin kudu maso kudu kuma ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewar za su goyi bayan dan takarar jam’iyyar AAC, Awara Biokpomabo, a yayin da su ke jiran hukuncin kotu a kan dan takarar jam’iyyar su.

A saboda haka a ranar Asabar, 9 ga wata, za mu zabi dan takarar jam’iyyar AAC. Ku koma azabunku ku zabi jam’iyyar AAC. Babu wani dalili da zai sa ku ki fita domin kada kuri’a, akwai tsaro. Ku yi shiri ku fita domin mu samu nasarar lashe zabe,” a cewar Amaechi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel