Da dumin sa: An cafke mutane 18 dake hada-hadar kawunan mutane a Najeriya

Da dumin sa: An cafke mutane 18 dake hada-hadar kawunan mutane a Najeriya

Rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Oyo dake a yankin Kudu maso yammacin Najeriya sun sanarwa da manema labarai samun nasarar su ta cafke wasu kasurguman masu aikata laifufuka a jihar cikin su hadda masu safarar kanun mutane har su 18.

Sauran laifuffukan da hukumar 'yan sandan sukace sun kama mutanen da aikatawa hadda fashi da makami, damfara da kuma karkatar da tankar mai dauke da man fetur a jihar.

Da dumin sa: An cafke mutane 18 dake hada-hadar kawunan mutane a Najeriya
Da dumin sa: An cafke mutane 18 dake hada-hadar kawunan mutane a Najeriya
Asali: Facebook

KU KARANTA: Ibrahim Shekarau ya fito a fim din Hausa

Legit.ng Hausa ta samu cewa kwamishinan 'yan sandan jihar Shina Plukolu ne ya bayyanawa manema labarai hakan yayin zantawar su a ofishin sa dake hedikwatar 'yan sandan a garin Ibadan, babban birnin jihar ta Oyo.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga magoya bayan sa da dukkan masu jefa kuri’a da su zabi ’yan jam’iyyar sa ta APC daga sama har kasa, domin hakan ne kadai zai taimaka ma sa wajen hanzarta cimma burinsa na Mataki na gaba, watau ‘Next Level’.

Shugaban kasar dai ya bayyana hakan ne ranar Laraba cikin wani sakonsa da ya aike ga ’yan Najeriya kan zaben da za a gudanar ranar 9 ga Maris, 2019 na gwamnoni da ’yan majalisun jihohi a dukkan fadin kasar in banda jahohi 7 kacal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel