Masu canjin kudi ne su ka sa mu ka yi ram da Yaran Atiku - EFCC

Masu canjin kudi ne su ka sa mu ka yi ram da Yaran Atiku - EFCC

Jaridar Vanguard ta bada labarin yadda masu canjin kudi su ka jefa yaran ‘dan takarar shugaban kasa na PDP watau Alhaji Atiku Abubakar cikin matsala bayan da aka same su da makudan kudin waje.

Masu canjin kudi ne su ka sa mu ka yi ram da Yaran Atiku - EFCC
EFCC ta kama Lauyan Atiku bayan an same sa Dalolin kudi
Asali: Facebook

Kama wasu jagororin yakin neman zaben Atiku Abubakar da aka yi kwanan nan bai rasa nasaba da makudan kudin kasar waje da aka samu a hannun su. Kamar yadda mu ka samu labari, EFCC ta same su ne da miliyoyin Daloli.

An kama babban Lauyan Atiku, Uyi Giwa Osagie, da kuma Surukin sa watau Alhaji Babalele Abdullahi ne bayan wasu jami’an hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa sun same su da tsabar kudi.

KU KARANTA: ‘Dan takara ya nemi a rusa takarar da Buhari da Atiku su kayi a zaben 2019

Wata majiya daga EFCC ta bayyana cewa wadannan mutane na-kusa da Atiku Abubakar sun dauki kudi har Dala miliyan 1.6 ne da niyyar canza su domin ayi amfani da su wajen zaben shugaban kasa da aka yi makonnin da su ka wuce.

Ma’aikatan na EFCC sun cafke mukarraban ‘dan takarar jam’iyyar adawar ne bayan sun samu labarin an shiga da kudi zuwa wajen wasu ‘yan canji a cikin yankin Lagos Island a jihar Legas. Yanzu haka dai an saki wasu da aka kama.

Lokacin da jami’an na EFCC su ka dura kasuwar da ke Legas, tuni har an canza kusan $140000 daga cikin kudin a kan N358, wannan ya bada dama aka samu Naira miliyan 50. An gaza canza sauran kudin ne saboda karancin Naira a kasuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel