Aiki dai Wakili: An damke dilolin kwaya 54 a jihar Kano

Aiki dai Wakili: An damke dilolin kwaya 54 a jihar Kano

- Hukumar yan sandan jihar Kano tayi babban kamu

- Kwamishana Muhammad Wakili ya fara aiki tukuru

Hukumar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama dilolin kwaya 54 a cikin birnin Kano.

Kakakin hukumar yan sandan, DSP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da wannan labarin ne a wata jawabi da ya saki a Kano ranar Laraba inda yace an damke dilolin ne a wurare daban-daban yayinda yan sanda suka kai simame.

Ya ce wasu daga cikin dilolin na ta'amuni da hodar Iblis, ganyen wiwi, madarar sukudaye, sholisho, taramol, da wasu muggan kwayoyi.

Haruna ya kara da cewa an damke wani Mujahid Abubakar da Iliya Garba a kasuwar Sabon Gari da jibgin kwayoyi.

Daga cikin kwayoyin da aka kwace sune: Kwayar Exol 5 -39000 tabs, Kwayar Sycozines 5 – 21000 tabs, Allurar Diazepam – kwalabe 166000, Allurar Tranzile -kwalabe 7000 , Allurar Tramadol – kwalabe 2150, allurar Ejon Merinetin – kwalabe 8000, Allurar Nart phenobartil – kwalabe 180, allurar penzozine – 40, Allurar Voltean – 14,da Kwayar C0cadamol – 1600.

Ya ce wadanda aka kama sun yi amannaa da laifin da ake tuhumarsu da shi kuma ana cigaba da kokarin fito da abokan aikinsu domin gurfanar da su a kotu.

KU KARANTA: Labaran waje: An samu sabani tsakanin Sarkin Saudiyya da Yarima mai jira gado MBS

Hakazalika, kakakin yan sandan ya tabbatar da damke wani Muhammed Abdullahi wanda ya shahara a dillancin hodar Iblis.

Muhammad Abdulllahi wanda mazaunin Hotoro ne ya shiga hannun hukuma ranar 28 ga watan Febrairu, 2019 da dunkulen hodar iblis hudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel