Dan takarar APC da ya fadi zaben kujerar majalisar wakilai ya koma PDP

Dan takarar APC da ya fadi zaben kujerar majalisar wakilai ya koma PDP

- Dan takarar majalisar tarayya na APC a mazabar Etinan, Dan Akpan ya fice daga jam'iyyar ya koma PDP

- Mr Akpan ya sanar da ficewarsa daga jamiyyar APC ne bayan ya sha kaye a zaben da aka gudanar a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu

- Shugaban kungiyar yakin neman zabe na Chris Ekpenyong ya shawarci Sanata Godswill Akpabio ya amince da kayen da ya sha

Tsohon dan takarar majalisar wakilai na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na mazabar Etinan, Dan Akpan da ya sha kaye a wurin Kakakin majalisar jihar Akwa Ibom Onofiok Luke a zaben da aka gudanar ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP.

Dan takarar APC da ya fadi zaben kujerar majalisar wakilai ya koma PDP
Dan takarar APC da ya fadi zaben kujerar majalisar wakilai ya koma PDP
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tarihi: Kyawawan hotunan shugabannin Najeriya 5 da matan su

Akpan ya fice daga jam'iyyar APC ne tare da Etido Ibekwe, tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar jihar daga karamar hukumar Udim tare da wasu 'yan siyasan sun koma PDP ne yayin kamfen din jam'iyyar da akayi a filin wasa na Uyo.

A yayin da ya ke jawabi a Uyo, Gwamna Udom Emmanuel na jihar ya kallubalanci abokin hammyarsa cewa suyi amfani da tsarin zabe na A4, inda ya ce idan anyi amfani dashi PDP ne za ta lashe zabe a jihar.

Ya ce, "Ina kallubalantar mutanen Abuja, idan sun san sun shirya su karaso zuwa Akwa Ibom, domin al'ummar Akwa Ibom suyi layi, idan sun sami 20%, kada ku sake yarda da mu idan mun ce muku PDP ta Akwa Ibom ne".

Direkta Janar na Divine Mandata Organization, Commodore Idongesit Nkanga (murabus) ya yi kira ga Sanata Godswill Akpabio ya amince da kaye ya kuma taya Chris Ekpenyong murnar lashe zabe inda ya ce hakan shine dattaku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel