Zaben Gwamna: Buhari ya yiwa al'ummar Najeriya jawabai na gargadi

Zaben Gwamna: Buhari ya yiwa al'ummar Najeriya jawabai na gargadi

Da sanadin kafar watsa labarai ta shafin jaridar Vanguard mun samu rahoton cewa, yayin ci gaba da karatowar zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki na jiha, a yammacin yau na Laraba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa daukacin al'ummar Najeriya jawabai.

A yau Laraba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabai ga daukacin al'ummar Najeriya yayin gabatowar babban zaben kujerar gwamnoni da kuma 'yan majalisun dokoki ta jiha da za a gudanar a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Zaben Gwamna: Buhari ya yiwa al'ummar Najeriya jawabai na gargadi
Zaben Gwamna: Buhari ya yiwa al'ummar Najeriya jawabai na gargadi
Asali: UGC

Shugaba Buhari cikin zayyana jawabai ya mika sakon sa na godiya da kuma jin-jina ga al'ummar kasar nan da suka dangwala masa kuri'u domin tabbatar da nasarar sa ta tazarce yayin zaben kujerar shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun da ya gabata.

Bayan bayyana takaicin sa da jajantawa wadanda rikici yayin zabe ya yi tasiri wajen salwantar rayuka da kuma jikkatar wasu daga cikin al'ummar kasar nan, shugaban kasa Buhari ya kuma gargadi a al'ummar da su kauracewa sanya hannu cikin duk wani nau'i na ta'ada da tarzoma.

KARANTA KUMA: Hadimin tsohon Gwamna Fayose ya sauya sheka zuwa APC

Buhari ya shawarci al'ummar Najeriya da su fito kwansu da kwarkwata wajen dangwala kuri'u bisa ga tanadi na dimokuradiyya da kuma shimfidar 'yancin su ta fuskar kundin tsarin mulki. Ya kuma fadakar akan zaben jagorori nagari wadanda suka cancanta.

Ya kuma jaddada matsayar sa da kuma akida ta gudanar da ingataccen zabe da ya tsarkaka daga duk wani nau'i na rashin gaskiya yayin da kasashen duniya suka sanya idanun lura kan al'amurran kasashen Afirka musamman Najeriya kasancewar ta madubin dubawa a nahiyyar Afirka.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel