Buhari ya sake jan kunnen masu satar akwatin zabe

Buhari ya sake jan kunnen masu satar akwatin zabe

A yau Laraba 6 ga watan Maris ne shugaba Muhammadu Buhari ya sake kira ga 'yan Najeriya su sake fitowa kwansu da kwarkwata su zabi 'yan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamnoni da 'yan majalisun jiha.

A cewarsa, za a baza jami'an tsaro a wuraren da suka dace domin tabbatar da zabe ya tafi lami lafiya.

A sakon da shugaban kasar ya bayar, ya ce zaben gwamnoni da 'yan majalisu da za a gudanar yana da muhimmanci kamar na shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.

DUBA WANNAN: APC ta soke ziyarar da Buhari zai kai zuwa wasu jihohin PDP 5

Buhari ya sake jan kunnen masu satar akwatin zabe
Buhari ya sake jan kunnen masu satar akwatin zabe
Asali: Facebook

A yayin da ya ke yiwa matasa gargadin kada su bari ayi amfani da su wurin tayar da zaune tsaye, ya kuma gargadi masu satar akwatin zabe da masu aikata sauran laifukan zabe su tuba daga aikata hakan.

Ya ce, "Zabe karo na biyu ne shekarar 2019 yana tafe a ranar Asabar 9 ga watan Maris inda 'yan Najeriya za su zabi gwamnoni da 'yan majalisun tarayya.

"Duk da cewa zaben shugaban kasa ya wuce, kada muyi kasa a gwiwa mu fito mu kada kur'un mu a zaben gwamnoni.

"Zaben da ke tafe yana da muhimmanci kamar yadda zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya ke da muhimmanci.

"Ina baku shawara ku fito kwanku da kwarkwata domin ku kada kuri'an ku.

"Ku guji duk wani halin rashin da'a aringizon kuri'a, satar akwatin zabe da duk wani halin rashin da'a da bai dace ba.

"Ina baku tabbacin cewa jami'an tsaro za su kasance a kasa domin tabbatar da cewa an gudanar da zabe cikin lafiya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel