Fara wa da iya wa: Atiku ya samu nasara ta farko a kotun sauraron karar zabe

Fara wa da iya wa: Atiku ya samu nasara ta farko a kotun sauraron karar zabe

Kotun daukaka kara ta umarci hukmar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta bawa dan takarar shugaban kasa da aka kayar a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu, Atiku Abubakar, da jam’iyyar sa, PDP, damar duba dukkan kayayyaki da aka yi amfani da su a zaben shugaban kasa.

Kotun mai alkalai uku karkashin jagorancin Abdul Aboki ta ce INEC ta bawa Atiku da PDP damar yin nazari da binciken kwakwafi a kan dukkan kayan da aka yi amfani da su a zaben.

Da ya ke karanto hukuncin da kotun yanke bisa amincewar alkalan uku, Mista Aboki, ya hana Atiku da PDP gudanar da bincike ta hanyar kimiyyar zamani (Forensiv analysis) a kan kayan aikin zaben da INEC za ta ba su don su duba.

Kazalika, kotun ta hana INEC bayar da kayan aikin zaben domin gudanar da bincike ta hanyar kimiyyar zamani a kan su.

Fara wa da iya wa: Atiku ya samu nasara ta farko a kotun sauraron karar zabe
Atiku
Asali: Twitter

Hari la yau, kotun ta hana masana bincike ta hanyar kimiyyar zamani su duba kayan aikin zaben, musamman fom din EC48 da wasu ragowar kayayyakin kamar yadda ma su shigar da kara su ka nema.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

DUBA WANNAN: INEC ta fadi matakin da za ta dauka a duk akwatin da ‘yan daba su ka hana amfani da na’ura

Mista Aboki ya bayyana cewar Chris Uche, lauyan wanda ya shigar, bai yi kuskure ba wajen neman kotun ta bawa wanda ya ke kare wa damar yin bicike ta hanyar kimiyya a kan kayan zaben bisa kafa hujja da hukuncin kotun sauraron karar zabe ta yi a baya. Sai dai, y ace yin hakan tamkar yi wa mai kara wata alfarma ce ta musamman.

Kotun daukaka karar ce ta maye gurbin kotun sauraron korafin zabe.

Atiku da jam’iyyar PDP na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairu da INEC ta bayyana shugaba Buhari a matsayin wanda ya yi nasara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel