Kotu ta kwace kujerar dan majalisar wakilai da aka zaba a APC, ta bawa PDP

Kotu ta kwace kujerar dan majalisar wakilai da aka zaba a APC, ta bawa PDP

Wata kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Yola, jihar Adamawa, ta umarci dan takarar kujerar majalisar wakilai na mazabar Yola ta Kudu da Girei da Yola ta Arewa, Abdurrauf Abubakar, da aka zaba a karkashin tutar APC da ya mika nasarar zaben da ya samu ga dan takarar jam’iyyar PDP, Jaafaru Sulaiman Ribadu.

Kotun ta yanke wannan hukunci bisa dogaro da hujjar cewar ba a gudanar da sahihin zaben cikin gida da samar da Abubakar ba, hakan ya sa ta yanke hukuncin mika kujerar ga Ribadu, dan takarar da ya zo na biyu a zaben kujerar majalisar wakilan tarayya da sanatoci da aka yi tare da na shugaban kasa a ranar 23 ga watan Fabrairu.

Kotun ta gwamnatin tarayya ta umarci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da karbi takardar shaidar samun nasara a zabe da ta bawa Abdurrauf, dan takarar jam’iyyar APC.

Kotu ta kwace kujerar dan majalisar wakilai da aka zaba a APC, ta bawa PDP
Kotu ta kwace kujerar dan majalisar wakilai da aka zaba a APC, ta bawa PDP
Asali: UGC

Alkalin kotun, Jastis Abdulaziz Anka, ya umarci Abdurrauf ya bar kujerar da aka zabe shi a ranar 23 ga watan Fabrairu domin bawa dan takarar da ya zo na biyu damar maye gurbin sa tunda ba a bi ka’ida wajen gudanar da zaben cikin gida da ya bashi tikitin tsaya wa takara ba.

Wakilin mazabar a majalisar wakilai, Lawal Abubakar Garba, wanda kuma dan jam’iyyar APC ne shine wanda ya shigar da karar bayan Abdurrauf ya kayar da shi a zaben cikin gida. Ya shigar da karar APC, Abdurrauf, da hukumar INEC.

DUBA WANNAN: Fara wa da iya wa: Atiku ya samu nasara ta farko a kotun sauraron karar zabe

"Ina mai umartar wanda ake kara na biyu (Abdurrauf) da ya bar kujerar da aka zabe shi ta wakilcin mazabun Yola ta Arewa da Yola ta Kudu da Girei a majalisar tarayya.”

“Ina mai umartar hukumar INEC da ta karbi shaidar samun nasarar lashe zabe da ta ba shi domin mika ta ga dan takarar da ya zo na biyu a zaben kujerar wakilcin mazabun a majalisar waiklai wanda aka gudanar da zabe ranar 23 ga watan Fabrairu.

“Wannan shine hukuncin da wannan kotu ta yanke. Duk wanda bai gamsu ba ya na da damar daukaka kara,” a cewar Jastis Anka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel