INEC ta fadi matakin da za ta dauka a duk akwatin da ‘yan daba su ka hana amfani da na’ura

INEC ta fadi matakin da za ta dauka a duk akwatin da ‘yan daba su ka hana amfani da na’ura

- Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana cewar amfani da na’urar tantance ma su zabe kafin kada kuri’a ya zama tilas

- Festus Okoye, kwamishinan yada labaran hukumar INEC, ya ce ba za a kidaya kuri’un akwatin da aka yi zabe ba tare da amfani da na’ura ba

- Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce sun buga kuri’u daidai da adadin mutanen da ke da rijistar zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce ba za a kirga kuri’un duk akwatin da ‘yan daba ko ‘yan bangar siyasa su ka hana amfani da na’urar tantance ma su kada kuri’u ba.

INEC ta kara da cewa za ta tabbatar da cewar an yi amfani da na’urar tantance ma su kada kuri’a a zaben gwamnoni da mambobin majalisun dokoki da za a yi a fadin jihohin 29 da ke kasar nan.

INEC ta fadi matakin da za ta dauka a duk akwatin da ‘yan daba su ka hana amfani da na’ura
Na’urar tantance ma su zabe
Asali: Facebook

Hukumar zaben ta bayyana haka ne ta bakin kwamishinanta na yada labarai da wayar da kan ma su kada kuri’a, Festus Okoye.

DUBA WANNAN: Nasarar Buhari: Matashi ya fara tattaki daga Kebbi zuwa Abuja

A nasa bangaren, shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewar sun bugo kuri’u daidai da yawan adadin ma su katin zabe a kowacce mazaba da ke fadin kasar nan.

Duk da akwai jam'iyyu fiye da 80 a Najeriya, zaben gwamnonin da za a yi ranar Asabar mai zuwa zai fi daukan hankali ne tsakanin jam'iyyar APC da PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel