Zaben Gwamna: Kungiyar magoya bayan Buhari ta amince da dan takarar jam'iyyar ADC a jihar Adamawa

Zaben Gwamna: Kungiyar magoya bayan Buhari ta amince da dan takarar jam'iyyar ADC a jihar Adamawa

Kungiyar Matasa magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari reshen Arewa maso Gabashin Najeriya, ta bayyana amincewar ta kan dan takarar kujerar gwamnan jihar Adamawa na jam'iyyar ADC, Abdul'aziz Nyako.

Yayin sabawa akidar siyasa ta jam'iyyar shugaban kasa Buhari da ta kasance jam'iyya mai ci ta APC, kungiyar matasa magoya bayan sa reshen Arewa maso Gabas ta shimfida goyon baya tare da bayyana sahalewar ta kan dan takarar gwamnan jihar Adamawa na jam'iyyar ADC.

Zaben 2019: Kungiyar magoya bayan Buhari ta amince da dan takarar jam'iyyar ADC a jihar Adamawa
Zaben 2019: Kungiyar magoya bayan Buhari ta amince da dan takarar jam'iyyar ADC a jihar Adamawa
Asali: Twitter

Jagoran kungiyar, Aliyu Usman Waziri, shine ya bayyana hakan a jiya Talata yayin ganawar sa da manema labarai cikin birnin Yola. Ya ce duba da cancantar Nyako kungiyar ta shimfida goyon baya ga jam'iyyar sa ta ADC yayin zaben gwamna da za a gudanar a ranar 9, ga watan Maris.

Waziri bayan goyon shugaban kasa Buhari na jam'iyyar APC yayin zaben kujerar shugaban kasa da aka gudanar makonni biyu da suka gabata, ya ce a halin yanzu kungiyar na goyon bayan dan takara na jam'iyyar ADC yayin zaben gwamna da za a gudanar a ranar Asabar mai gabatowa.

KARANTA KUMA: Zaben Gwamna: An fara jigilar kayayyakin zabe a jihar Kano

Shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, kungiyar ta yi watsi da dan takarar kujerar gwamnan jihar Adamawa na jam'iyyar APC, Gwamna Muhammadu Jibrilla, sakamakon yadda gwamnatin sa ta gaza inganta harkokin kiwon lafiya da wasu muhimman bangarori tsawon shekaru hudu da ya shafe a bisa karagar mulki.

Waziri ya kara da cewa, kungiyar ta yanke wannan hukunci bisa ga madogara wajen ribatar shawarar shugaban kasa Buhari ta neman magoya baya su zabi cancanta wajen dangwala kuri'un su yayin babban zaben kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel