Dan majalisa Yusuf Buba na hararar kujerar kakakin majalisar wakilai Dogara

Dan majalisa Yusuf Buba na hararar kujerar kakakin majalisar wakilai Dogara

Mista Yusuf Buba, mamba, mai wakiltan Hong/Gombi na jihar Adamawa a majalisar wakila, ya bayyana sha’awarsa na son maye gurbin Yakubu Dogara a matsayin kakakin majalisan wakilai.

Mista Nkem Anyata-Lafiya, daraktan labarai na kungiyar Buba for Speaker Campaign Organisation (HYBYSCO 2019), ya bayyana hakan a wani jawabi a ranar Laraba, 6 ga watan Maris a Abuja.

A cewar Anyata-Lafia, Buba ya bayyana hakan ne a lokacin da mambobin kungiyar Igbos for One Nigeria (IFON) suka ziyarce shi domin taya shi murna akan nasarar da ya samu a zaben yan majalissu da aka gudanar.

Dan majalisa Yusuf Buba na hararar kujerar Kakakin majalisar wakilai Dogara
Dan majalisa Yusuf Buba na hararar kujerar Kakakin majalisar wakilai Dogara
Asali: Twitter

An tattaro inda Buba ke bayyana sha’awar sa na son neman matsayin kakakin majalisa idan aka kaddamar da yan majalisar a watan Yuni.

Har ila yau, Buba ya sha alwashin cewa yan mazabar sa da Najeriya za su ci amfanin gwamnatinsa, yayinda yake mika godiya ga al’umman mazabarsa akan yarda suka goya masa baya a lokacin zabe.

KU KARANTA KUMA: Zan zage damtsen aiki sosai a wannan karon - Buhari

Ya bayyana cewa shirinsa a matsayin kakakin majalsar zai kawo hadin kai. Har ila yau ya bayyana cewa dukkan yan majalisan zasu kasance cikin dukkan al’amura dake gudana a majalisan

Dan majalisan ya taya shugaban kasa Muhammadu Buhari, da yan majalissu da suka yi nasara a zabe murna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel