Nasarar Buhari: Matashi ya fara tattaki daga Kebbi zuwa Abuja

Nasarar Buhari: Matashi ya fara tattaki daga Kebbi zuwa Abuja

Wani masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC, Tukur Aliyu, ya fara tattaki daga Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi, zuwa Abuja domin nuna murnar sa da lashe zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabarairu da Buhari ya yi.

Aliyu, matashi mai shekaru 20 na haihuw, dan asalin karamar hukumar Argungu ta jihar Kebbi ne.

Da ya ke Magana da manema labarai kafin ya fara tattakin, Aliyu y ace tuntuni ya ci al washin cewar zai yi tattaki zuwa Abuja matukar shugaba Buhari ya lashe zaben kujerar shugaban kasa.

Na dauki alkawarin cewar zan yi tattaki daga Kebbi zuwa Abuja idan APC ta lashe zaben kujerar shugaban kasa. Zan yi tattakin ne saboda jam’iyya ta, APC, da goni na, Buhari,” a cewar Aliyu.

Matashin ya ce ya dauki garin kwaki, sukari, waken gwangwani, kosai a cikin jakar sa da kuma kudi N1,500 a matsayin guzurin da ya ke da bukata domin yin tattakin.

Nasarar Buhari: Matashi ya fara tattaki daga Kebbi zuwa Abuja
Buhari
Asali: Facebook

Buri na idan na karasa Abuja na gana shugab Buhari domin na yi ma sa murnar lashe zaben da ya yi,” a cewar matashin.

DUBA WANNAN: Ka nuna wa duniya takardar shaidar kai injiniyan gaske ne – Ganduje ya caccaki Kwankwaso

Kazalika, ya bukaci dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da Buhari ya kayar, da ya rungumi kaddara domin a samu zaman lafiya da cigaban kasa.

Ya yi kira ga dukkan magoya bayan jam’iyyar PDO da su yarda da ikon Allah su yi aiki da kiran da manyan kasar nan ke yi na su amince da sakamakon zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel