Yanzu Yanzu: Ana ta harbin bindiga yayinda magoya bayan APC da PDP suka kara a Nasarawa

Yanzu Yanzu: Ana ta harbin bindiga yayinda magoya bayan APC da PDP suka kara a Nasarawa

- Magoya bayan jam’iyyun All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) sun kara a jihar Nasarawa

- Anyi harbe-harben bindiga da dama wanda yayi sanadiyar lalata ababen hawa

- Rikicin ya kaure ne lokacin da magoya bayan jam’iyyun biyu ke jiran isowar yan takararsu yayinda ake shirin rufe kamfen din yan takarar gwamna da na majalisar dokokin jiha a gobe

Anyi harbe-harben bindiga da dama yayinda magoya bayan jam’iyyun All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) suka kara a garin Aqwatashi da ke karamar hukumar Obi a jihar Nasarawa.

Yanzu Yanzu: Ana ta harbin bindiga yayinda magoya bayan APC da PDP suka kara a Nasarawa
Yanzu Yanzu: Ana ta harbin bindiga yayinda magoya bayan APC da PDP suka kara a Nasarawa
Asali: Depositphotos

Majiyarmu ta ruwaito cewa rikicin ya kaure ne lokacin da magoya bayan jam’iyyun biyu ke jiran isowar yan takararsu yayinda ake shirin rufe kamfen din yan takarar gwamna da na majalisar dokokin jiha a gobe Alhamis.

Koda dai babu wanda aka rahoto cewa ya mutu, majiyarmu ta lura cewa harbin bindigan ya lalata ababen hawa da ke yiwa Shugaban karamar hukumar Obi rakiya.

KU KARANTA KUMA: Dan majalisa Yusuf Buba na hararar kujerar kakakin majalisar wakilai Dogara

A wani lamari na dabanm, Legit.ng ta rahoto cewa babban hafsan sojin Najeriya, Laftana Janar Tukur Buratai, a ranar Laraba, ya bayyana cewa hukumar sojin ta gano shirin da wasu yan siyasa ke yi domin tayar da hankali ranar zabe wanda ya hada da sanya bama-bamai.

Ya bayyana hakan ne yayi ganawarsa da kwamandoji, manyan hafoshi da diraktoci a hedkwatan soji dake birnin tarayya, Abuja. Yace binciken leke asiri da aka gudanar na nuna cewa wasu yan siyasa suna shirye-shiryen hana zaman lafiya yayin zaben gwamnoni da yan majalisun dokokin jiha.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel